Harin Bam: Rundunar Sojojin Najeriya ta Fadi Yadda Za Ta Yi da 'Yan Ta'adda

Harin Bam: Rundunar Sojojin Najeriya ta Fadi Yadda Za Ta Yi da 'Yan Ta'adda

  • Hedikwatar tsaron kasar nan ta bayyana adadin wadanda suka rasu a harin kunar bakin wake da aka kai Gwoza a jihar a Borno zuwa 20
  • Manjo Janar Edward Buba ne ya bayyana haka, inda ya kara da cewa mutane 52 ne suka ji mugayen raunuka kuma suna karbar magani
  • Edward Buba ya tabbatar da matsayar da suka cimma na daukar hukunci ta hanyar kawo karshen 'yan ta'addan cikin kankanin lokaci

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Abuja- Hedikwatar tsaro ta Najeriya ta bayyana cewa an samu karuwar wadanda suka rasu a harin da 'yan ta'adda su ka kai Gwoza.

Zuwa yanzu, an tabbatar da rasuwar mutane 20, yayin da wasu 52 su ka samu mugayen raunuka kuma yanzu haka suna karbar magani.

Kara karanta wannan

Tsaro: Sabon kwamishinan 'yan sandan Kano ya umarci sintirin jami'ai babu kakkautawa

Sojoji
Rundunar kasar nan za ta kawo karshen yan ta'adda Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Twitter

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa hedikwatar tsaron kasar nan za ta mayarwa 'yan ta'addan zazzafan martani cikin kankanin lokaci.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Za mu yi maganin yan ta'adda," DHQ

Rundunar sojojin kasar ta bayyana shirin maganin 'yan ta'addan da su ka kai mummunan hari Gwoza a jihar Borno har ya kashe mutane 20.

Hedikwatar tsaron kasar nan (DHQ) ta ce za ta tabbatar da kashe 'yan ta'addan da suka kai harin ba tare da bata lokaci ba.

Jaridar Leadership ta wallafa cewa daraktan yada labarai na hedikwatar, Manjo Janar Edward Buba ya ce 'yan kunar bakin wake uku ne suka tayar da bama-baman.

Ya ce an yi nasarar dakile hari na hudu bayan an gano mai dauke da bam din da wuri, wanda ya hakan ya sa ta kashe kanta ita kadai.

Sojoji sun hallaka 'yan bindiga

Kara karanta wannan

Tura ta kai bango: Mazauna Kaduna sun fatattaki 'yan ta'adda, an rage mugun iri a gari

A wani labarin, kun ji cewa sojojin kasar nan sun kashe akalla 'yan bindiga 188 tare da kama wasu 330 da ake zargi da kawo tarnaki a kasar nan.

Daraktan yada labaran hedikwatar, Manjo Janar Edward Buba, ya bayyana cewa wannan alama ce na cewa za a kawo karshen ta'addanci a Najeriya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.