Yaki da Ta’addanci: Kwastam Ta Kama Kwantena Makare da Makamai Daga Turkiyya

Yaki da Ta’addanci: Kwastam Ta Kama Kwantena Makare da Makamai Daga Turkiyya

  • Bashir Adeniyi, shugaban hukumar kwastam ta ƙasa, ya ce an kama manyan makamai da ƙwayoyi a tashar jirgin ruwa
  • Adeniyi ya sanar da manema labarai cewa darajar ƙwayoyin da makaman sun kai Naira biliyan hudu idan aka hada su
  • Rahotanni sun bayyana cewa, an ɓoye kayayyakin ne a cikin gwanjon kaya da aka shigo dasu daga ƙasar Turkiyya

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Rivers - Shugaban hukumar kwastam na ƙasa, Bashir Adeniyi, ya bayyana tarin makamai da harsasai da aka shigo dasu daga ƙasar Turkiyya.

Bashir Adeniyi ya ce an kama makaman ne da aka boye su a wata kwantena mai tsayin taku 40 da aka ƙwace a tashar jirgin ruwa ta Onne da ke Ribas.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya yi Allah wadai da harin bam a Borno, ya fadi matakin dauka

Kwastam sun ƙwace makamai da miyagun ƙwayoyi a Ribas. Hoto daga Hukumar Kwastam
Kwastam Sun Ƙwace Makamai Masu Darajar N2bn Daga Turkiyya
Asali: Facebook

Kwastam ta kwace makamai masu yawa

Hakazalika, an kama wasu miyagun ƙwayoyi da darajarsu ta kai Naira biliyan biyu, yayin da makaman suma darajarsu ta kai Naira biliyan biyu, jaridar Punch ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, an ɓoye ƙwayoyin da makaman ne cikin kayan gwanjon da aka shigo da su kasar daga Turkiyya.

An ruwaito cewa jami'an hukumar sun zage damtse a 'yan kwanakin nan kan kayayyakin da ake shigowa da su kasar, yayin da matsalar tsaro ke ci gaba da ta'azzara a kasar.

An kama mutane 3 da safarar makamani

A yayin bada bayanan kwantenar, shugaban hukumar Kwastam ya ce:

"Mun tattara bayanai sosai a kan kayayyakin da muka kama, mun dade muna bibiyar kontenonin bayan samun bayanan sirri a nan gida da kuma waje."

Kara karanta wannan

Shehu Sani ya fadi abin da shugabannin Arewa ya kamata su mayar da hankali a kai

A cewar Adeniyi, mamallakin kwantenar ya yi duk ƙoƙarin da zai yi na ɓoye miyagun kayayyakin da ya shigo dasu amma hakan ya gagara.

Shugaban ya bayyanawa manema labarai cewa an kama mutane uku da ake zargi da hannu a shigo da kayayyakin, kuma za a gurfanar da su idan an kammala bincike.

Sun kuma tsaresu bayan samun takardar amincewa tsaresu daga kotu.

Kwastam ta tatso harajin biliyan 10

A wani labari na daban, mun ruwaito cewa hukumar kwastam ta ƙasa ta sanar da gagarumar nasarar da ta samu na tattarawa gwamnatin Najeriya harajin Naira biliyan 10 a cikin watanni biyar kacal.

Hukumar ta sanar da hakan ne ta bakin shugabarta da ke reshen jihar Kwara mai suna Faith Ojeifo, wadda ta ce hukumar na kokarin cimma muradin gwamnati kan samar da haraji.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel