Sarkin Damaturu Ya Fara Yunkurin Rage Farashin Abinci Domin Saukakawa Talaka
- Al'ummar Najeriya na cigaba da kokawa kan yadda kayan masarufi suke kara tashin gauron zabi a kusan dukkan kasuwannin kasar
- Mai martaba sarkin Damaturu, Dakta Shehu Hashimi ibn Umar El-Kanemi ya fara ƙoƙari kan ganin al'umma sun samu sauki a Najeriya
- Legit ta tattauna da wata mai harkar saye da sayarwa a jihar Yobe, Aisha Jibril domin jin ko yan kasuwa sun karbi maganar sarkin garin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Yobe - Mai martaba sarkin Damaturu, Dakta Shehu Hashimi ibn Umar El-Kanemi ya yi kira ga yan kasuwa a jihar Yobe.
Sarkin ya yi magana ne yayin da kayan abinci suka yi tsada kuma suke ƙoƙarin gagarar talakawa a Najeriya.
Jaridar Leadership ta ruwaito cewa mai martaba Dakta Abubakar Hashimi ibn Umar El-Kanemi ya yi kiran ne a fadarsa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sarki ya roki a sauke farashi
Mai martaba sarkin Damaturu Dakta Shehu Hashimi ibn Umar El-Kanemi ya bukaci yan kasuwa su sauke farashin kayan abinci.
Sarkin ya ce a halin da ake ciki na tsadar kayayyaki ya sanya shi cikin damuwa ganin yadda talakawa ke shan wahala.
Dalilin neman sauke farashi
Shehu Hashimi ibn Umar El-Kanemi ya ce sauke farashin zai taimaka wajen kawo mafita ga halin tsanani da al'umma ke ciki.
Sarkin ya kara da cewa sauke farshin har ila yau zai kara taimakawa masu ƙaramin karfi wajen samun abinci cikin sauki.
El-Kanemi: 'Kuci riba 'yar kaɗan'
Sarkin Damaturu ya kara kira ga yan kasuwa kan rage cin kazamar riba domin hakan na jefa talakawa cikin wahala.
El-Kanemi ya kara da cewa cin riba mai yawa a kasuwanci ya sabawa hali na gari da ɗabi'a mai kyau, rahoton Daily Post.
Legit ta tattauna da Aisha Jibril
Wata mai saye da sayarwa, Aisha Jibril ta bayyanawa Legit cewa har yanzu ba bu wata alama da take nuna cewa an karbi umurnin sarkin Damaturu.
Aisha ta ce a halin yanzu farashin kayan masarufi kara haurawa sama yake a kasuwannin jihar kamar dai ba a yi kira ayi sauki ba.
Za a kayyade farashi a Najeriya
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Najeriya ta ce ta shirya tsaf don kayyade farashin kayan abinci a kasar yayin da hauhawar farashin kayan abinci ke kara kamari.
Ministan noma da tsaron abinci, Abubakar Kyari, ne ya bayyana hakan a kwanan nan kuma ya ce an nome karin filaye a fadin Najeriya.
Asali: Legit.ng