Jerin Jami'o'in Najeriya 7 da Mata Ke Jan Ragamar Shugabancinsu

Jerin Jami'o'in Najeriya 7 da Mata Ke Jan Ragamar Shugabancinsu

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

FCT, Abuja - A ɓangaren ilmi, an ba wasu mata ragamar jagorantar manyan jami'o'i domin nuna irin ta su gogewar da basira wajen shugabanci.

Matan sun zama kallabi tsakanin rawuna inda suke kafa tarihi da nuna ƙwarewa wajen gudanar da nauyin da aka ɗora a wuyansu.

Matan da ke shugabantar jami'o'i a Najeriya
Farfesa Aisha Maikudi ta zama shugabar riko ta jami'ar UniAbuja Hoto: UNIBEN, UNILAG, UniAbuja
Asali: Facebook

Matan da ke shugabantar jami'o'i a Najeriya

Legit.ng ta tattaro wasu matan Najeriya da ke jan ragamar shugabancin wasu jami'o'i a ƙasar nan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ga jerinsu a nan ƙasa:

Farfesa Aisha Sani Maikudi - Jami'ar UniAbuja

Farfesa Aisha Sani Maikudi ita ce shugabar riƙo ta jami'ar Abuja (UniAbuja).

Kara karanta wannan

Tsohon sanata ya fadi kuskuren Buhari da ya kamata Tinubu ya kiyaye

An naɗa Farfesa Aisha mai shekara 41 a duniya a muƙamin ne bayan Farfesaa AbdulRasheed Na’Allah ya kammala wa'adinsa a matsayin shugaban jami'ar na shida, cewar rahoton jaridar Leadership.

Farfesa Folasade Ogunsola - Jami'ar UNILAG

Farfesa Folasade Ogunsola ita ce shugabar jami'ar jihar Legas (UNILAG) ta 13 a tarihi.

Farfesa Folasade ita ce mace ta farko da ta taɓa shugabantar jami'ar a shekara 60 na tarihin kafuwarta.

Farfesa Folasade Ogunsola, wacce ɗiya ce a wajen Farfesa Akin Mabogunje, ta riƙe muƙamai masu yawa a jami'ar kafin ta zama shugaba.

Farfesa Lilian Salami - Jami'ar UNIBEN

Farfesa Lilian Salami ita ce shugabar jami'ar Benin (UNIBEN) da ke jihar Edo ta 10 a tarihi.

An haife ta ne a Jos, jihar Plateau a ranar, 8 ga watan Agustan 1956.

An naɗa Farfesa Lilian Salami a matsayin mace ta biyu da za ta shugabanci jami'ar bayan ƙarewar wa'adin Grace Alele Williams, wacce ita ce mace ta farko da ta taɓa shugabantar jami'a a Najeriya.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya yi Allah wadai da harin bam a Borno, ya fadi matakin dauka

Farfesa Florence Obi - Jami'ar UNICAL

Farfesa Florence ita ce shugabar jami'ar Calabar (UNICAL) ta 11 a tarihi. Ita ce mace ta farko da ta taɓa shugabantar jami'ar a cikin shekara 45 da kafa ta.

An naɗa Farfesa Florence a kan muƙamin ne a ranar, 10 ga watan Satumban 2020, inda ta maye gurbin Farfesa Zana Akpagu, wanda ya kammala wa'adinsa a ranar, 30 ga watan Nuwamban 2020.

Farfesa Nnenna Oti - Jami'ar FUTO

Farfesa Nnenna Oti ta zama shugabar jami'ar fasaha ta Owerri (FUTO), bayan ta yi nasara a kan sauran ƴan takara shida.

Ita ce shugabar jami'ar ta 11 kuma mace ta farko da ta taɓa riƙe muƙamin a cikin shekara 41 da kafa ta.

Farfesa Ibiyemi Bello - Jami'ar LASU

Farfesa Ibiyemi Olatunji-Bello, ita ce shugabar jami'ar jihar Legas (LASU) ta tara a tarihi.

Ita ce mace ta biyu da ta taɓa ɗarewa kan kujerar shugabancin jami'ar wacce ta ke mallakin jihar Legas.

Kara karanta wannan

Fulani makiyaya sun yi magana kan batun tsige Sarkin Musulmi, sun yi gargadi

Farfesa Ibiyemi wacce ke da shekara 57, ita ce matar tsohon kwamishinan muhalli da albarkatun ruwa na jihar Legas, Tunji Bello.

Farfesa Kaletapwa Farauta - Jami'ar ADSU

Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri na jihar Adamawa ya amince da naɗin Farfesa Kaletapwa Farauta a matsayin shugabar jami'ar jihar Adamawa da ke Mubi (ADSU) a shekarar 2020.

Kafin a yi mata wannan naɗin, ita ce shugabar riƙo ta jami'ar. Ta kuma taɓa riƙe muƙamin kwamishiniyar ilmi ta jihar Adamawa daga watan Agustan 2015 zuwa watan Yulin 2017.

Daga nan sai gwamnan jihar Adamawa, Sanata Muhammad Jibrilla Bindow ya naɗa ta shugabar riƙo ta jami'ar ADSU a ranar 17 ga watan Yulin 2017, cewar rahoton jaridar PM News.

Gwamna ya sauya sunan jami'a

A wani labarin kuma, kun ji cewa Gwamna Bala Mohammed ya amince da sauya sunan jami’ar jihar Bauchi da ke Gadau zuwa Jami’ar Sa’adu Zungur (SAZU).

Kara karanta wannan

An ba alkalai cin hanci a shari'ar zaben shugaban kasa na 2023? Gaskiya ta bayyana

Gwamna Bala ya rattaɓa hannu kan ƙudirin dokar sauya sunan jami'ar bayan majalisar dokokin jihar Bauchi ta amince da shi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel