Kotu ta yi Fatali da Karar da Shugaban IPOB, Nnamdi Kanu ya Shigar kan Gwamnati

Kotu ta yi Fatali da Karar da Shugaban IPOB, Nnamdi Kanu ya Shigar kan Gwamnati

  • Babbar kotun tarayya a Abuja ta yanke hukunci kan karar da shugaban haramtacciyar kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu ya shigar gabanta
  • Nnamdi Kanu, wanda gwamnati ke zargi da laifukan cin amanar kasa na jagorantar tafiyar Biafra da ke neman ballewa daga Najeriya
  • Mai shari'a James Omotosho ya yi watsi da tuhumar da Kanu ke yiwa gwamnatin tarayya na kin yi masa adalci a shari'ar da ake yi

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Abuja- Babbar kotu da ke zamanta a Abuja ta yanke hukunci kan karar da daurarren shugaban haramtacciyar kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu ya shigar gabanta.

Nnamdi Kanu, ta bakin lauyoyinsa ya shigar da gwamnatin tarayya da hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) kotu ya na neman a biya shi diyyar N1bn.

Kara karanta wannan

Lauyoyin Yahaya Bello sun shiga uku, hukumar EFCC ta roƙi kotu ta ɗaure su

Nnamdi Kanu
Kotu ta kori karar da Nnamdi Kanu ya shigar Hoto: Marco Longari
Asali: Getty Images

Nigerian Tribune ta tatatro cewa mai shari'a, James Omotosho a yau ya yi fatali da karar ta Nnamdi Kanu saboda gaza nunawa kotu bukatar haka.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Babu shaidar DSS ta shiga hurumin Kanu," Kotu

Mai shari'a James Omotosho ya kori karar da Nnamdi Kanu ya shigar ya na kalubalantar hukumar DSS da yi masu kutse da sauraron bayanai tsakaninsa da lauyoyinsa a sirrance.

Jaridar Punch ta wallafa cewa da ya ke yanke hukuncin, alkalin ya bayyana cewa Mista Kanu ya gaza kawo hujjojin da za su tabbatar da zarge-zargen da ya yi.

Haka kuma mai shari'a Omotosho ya jaddada cewa lauyoyin Kanu sun gaza tabbatar da hujjojinsu na zargin kin yi masu adalci a shari'ar da ake gudanarwa.

Kotu ta hana belin Nnamdi Kanu

A wani labarin kun ji cewa babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta ki bayar da belin shugaban haramtacciyar kungiyar ta IPOB, Nnamdi Kanu.

Kara karanta wannan

Jihohi 3 da ke zargin gwamnatin tarayya da yi masu katsalandan

Haka kuma mai shari'a Binta Nyako ta nemi a gaggauta ci gaba da shari'ar da ake yi tsakaninsa da gwamnatin Najeriya kan cin amanar kasa da tayar da zaune tsaye.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.