'Yan Boko Haram Sun Kwararo Zuwa Jihar Neja Daga Kasashen Waje? An Gano Gaskiya

'Yan Boko Haram Sun Kwararo Zuwa Jihar Neja Daga Kasashen Waje? An Gano Gaskiya

  • An yi ta yaɗa wasu rahotanni masu nuna cewa ƴan ta'addan Boko Haram daga Jamhuriyar Nijar da Jamhuriyar Benin sun kwararo zuwa jihar Neja
  • Mazauna garin New Bussa sun fito sun bayyana cewa ko kaɗan babu ƙamshin gaskiya a batun zuwan ƴan ta'addan a yankin
  • Rahoton ɓullar ƴan ta'addan dai da farko ya jefa firgici a zukatan mutanen yankin amma yanzu sun koma gudanar da harkokinsu na yau da kullum

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Neja - Mazauna garin New Bussa da ke ƙaramar hukumar Borgu a jihar Neja sun ƙaryata batun kwararowar ƴan ta’adda daga jamhuriyar Nijar da jamhuriyar Benin zuwa yankin.

A makonni da suka gabata ne wani faifan bidiyo ya yi ta yawo a kafafen sada zumunta wanda ke nuna yadda wasu gungun ƴan ta'adda masu alaƙa da Boko Haram da Al-Qaeda ke barazanar mamaye gandun dajin Kainji.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da 'yan bindiga suka sace basarake da wasu bayin Allah a Arewa

'Yan ta'addan Boko Haram ba su shiga Neja ba
An musanta batun kwararowar 'yan ta'addan Boko Haram zuwa jihar Neja
Asali: Original

Lamarin ya haifar da fargaba ga mazauna garin New Bussa, hedkwatar ƙaramar hukumar Borgu da garuruwan da ke makwabtaka da shi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Menene gaskiyar zuwan ƴan ta'adda a Neja?

Da yake zantawa da jaridar Daily Trust, kakakin ƙungiyar BYDA, Yakubu Aliyu Bio, ya bayyana cewa ko da ƴan ta’adda suna yin amfani da wasu sassan dajin na Kainji a matsayin maɓoya, rahoton kwararowar ba shi da tushe balle makama.

"Tun da farko jami’an tsaro sun tabbatar da cewa labarin ƙarya ne. Ko da yake an samu babban firgici da farko, shugaban gandun danjin wanda ɗan asalin yankin ne, ya tabbatar da cewa labarin ba gaskiya ba ne."
"Tuni dai mazauna garin suka koma harkokinsu na yau da kullum."

- Yakubu Aliyu

Wani mazaunin garin Yahaya Abdulsamad, ya nuna cewa ƴan ta'adda sun yiwa yankin barazana a baya, amma ya jaddada cewa, rahoton da aka samu na kwararowar ƴan ta'addan daga Nijar da Benin ba gaskiya ba ne.

Kara karanta wannan

Dakarun sojojin sama sun yi ruwan wuta kan 'yan ta'adda da barayin man fetur

"A shekarar da ta gabata, ƴan ta’adda sun yi yunƙurin kai hari a barikin sojoji. Yayin da akwai rahotannin ƴan ta'adda na ɓoyewa a kusa da New Bussa, batun kwararowar ƴan ta'adda daga Nijar da Benin ba gaskiya ba ne."

- Yahaya Abdulsamad

Sojoji sun yi nasara kan ƴan ta'adda

A wani labarin kuma, kun ji cewa hedikwatar tsaro ta ƙasa (DHQ) ta bayyana cewa, dakarun sojoji da ke aikin samar da tsaro a faɗin ƙasar nan sun kuɓutar da mutum 1,993 da aka yi garkuwa da su.

Dakarun sojojin sun kuma kashe ƴan ta'adda 2,245 tare da cafke mutum 3,682 da ake zargin ƴan ta'adda ne cikin watanni uku.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel