Tashin Hankali Yayin da Yan Bindiga Suka Sace Basarake da Wasu Bayin Allah a Arewa
- Ƴan bindiga sun yi awon gaba da dagacin Tunburku, Malam Ashiru Sharehu a ƙaramar hukumar Giwa ta jihar Kaduna
- Mazauna garin sun bayyana cewa maharan sun tafi da basaraken a lokacin da ya kamo hanyar dawowa gida daga gonarsa ranar Asabar
- Haka nan kuma wasu ƴan bindiga sun yi garkuwa da manoma biyu suna tsakiyar aiki a gonakinsa a Sabon Layi da ke gundumar Kidandan
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kaduna - 'Yan bindigan daji sun yi garkuwa da magajin garin Tunburku da ke karamar hukumar Giwa a jihar Kaduna, Malam Ashiru Sherehu.
Rahotanni sun bayyana cewa Malam Ashiru ya faɗa hannun masu garkuwa ne a lokacin da yake hanyar dawowa daga gona ranar Asabar.
Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa ƴan fashin daji sun addabi garin wanda ke ƙarƙashin gundumar Fatika a ƴan kwanakin nan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wani mazaunin garin mai suna Ahmadu ya ce a halin yanzu manoma ba su iya zuwa gonakinsu da ke bayan gari saboda fargabar hare-haren ƴan fashin daji.
Yadda aka sace basarake a Kaduna
Hussaini Umar, wani shugaban al'umma a yankin wanda ke riƙe da sarautar Sarkin Fadan Galadimawa ya tabbatar da sace basaraken ga manema labarai.
Ya ƙara da cewa maharan sun yi awon gaba da Magajin Garin da misalin karfe 5:00 na yammacin ranar Asabar, rahoton Guardian.
"Yana hanyar dawowa daga gonarsa da ke a nan yankin Tunburku kwatsam ƴan fashin suka tare shi, suka tafi da shi cikin jeji.
"Har kawo yanzu ba mu ji daga waɗanda suka yi garkuwa da shi ba, ba su tuntuɓe mu ba tukunna," in ji shi.
Yan bindiga sun sace manoma
A cewar Hussaini, an sace wasu manoma biyu a Sabon Layi da ke karkashin gundumar Kidandan a lokacin da suke aiki a gonakinsu ranar Lahadi da rana.
Ya ce mutanen da lamarin ya faru a kan idonsu ba su iya tunkarar ƴan bindigar ba saboda suka ɗaukeda makamai.
Ya yaba da kokarin sojojin da aka tura yankin amma ya roki gwamnati da ta aike da ƙarin jami’an tsaro da yawa saboda matsalar tsaro.
Yadda aka sace shanun liman a Kaduna
Kuna da labarin ƴan bindiga sun kai hari kauyen Gidan-Makera a ƙaramar hukumar Kagarko da ke jihar Kaduna, sun tafi da shanun babban limamin garin.
Mazauna yankin sun bayyana cewa wasu ƴan banga sun yi nasarar kwato shanun bayan sun bi bayansu ranar Talata.
Asali: Legit.ng