Gwamnatin Zamfara Ta Watsawa Tinubu Kasa a Ido, Ta Yi Fatali da Matakin da Ya Dauka
- Bayan Shugaba Bola Tinubu ya nada sababbin sakatarorin din-din-din, jihar Zamfara ta yi fatali da mai wakiltarta
- Gwamnatin jihar ta ki amincewa da nadin Dakta Maryam Ismaila Keshinro wacce za ta wakilci jihar
- Tinubu ya nada sababbin sakatarorin ne guda takwas cikin har da Maryam a ranar Juma'a 28 ga watan Yunin 2024
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Zamfara - Gwamnatin jihar Zamfara ta ki amincewa da nadin da Bola Tinubu ya yi na wata 'yar jihar a Abuja.
Gwamnatin ta ki amincewa da nadin Maryam Ismaila Keshinro a matsayin sakatariyar din-din-din daga jihar.
Tinubu ya nada Maryam mukami daga Zamfara
Tinubu ya sanar da nadin Maryam tare da wasu bakwai a matsayin sakatarorin kamar yadda Ajuri Ngelale ya tabbatar a ranar Juma'a 28 ga watan Yunin 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai Zamfara ta yi fatali da nadin inda ta ce Maryam ba asalin 'yar jihar ba ce domin haka ba ta cancanci wakiltarta ba.
A cikin wata takarda da Premium Times ta leko, shugaban ma'aikatan gwamnatin jihar, Ahmad Liman ya tabbatar da cewa Maryam ba 'yar asalin jihar ba ce.
Martanin gwamnatin Zamfara kan nadin Maryam
"Wanda aka nadan ba 'yar asalin jihar Zamfara ba ce domin haka ba ta cancanki wakiltarta ba ko kuma samun wata dama dalilin jihar."
"Dalilin haka, babu wasu takardu da ke tabbatar da ita ko kuma bata damar wakiltar jihar Zamfara ta kowace fuska."
- Cewar sanarwar
Sanarwar ta kara da cewa ana yawan nuna wa jihar warayya daga Gwamnatin Tarayya sannan nadin Maryam ya kara tabbatar da kukan da suke yi.
Maryam dai ta kasance likitar yara ce da take da kwarewar aiki har na tsawon shekaru fiye da ashirin a matakai daban-daban.
An taso Dauda Lawal a gaba a Zamfara
A wani labarin, kun ji cewa ana cigaba da sukan Gwamna Dauda Lawal bisa aniyar gina katafaren filin jirgin sama a jihar.
Gwamna Dauda Lawal zai kashe kudi kimanin Naira biliyan 62.8 domin gina filin da sauKar jiragen sama a birnin Gusau.
Asali: Legit.ng