Borno: Adadin Mutanen da Suka Rasu Sakamakon Harin Kunar Bakin Wake Ya Karu
- Ƴan ƙunar baƙin wake sun kai hare-haren bam a ƙaramar hukumar Gwoza ta jihar Borno a ranar Asabar, 29 ga watan Yunin 2024
- Ƴan ƙunar baƙin waken sun yi sanadiyyar rasuwar mutum 18 yayin da wasu da dama suka samu munanan raunuka
- Shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar (SEMA) wanda ya tabbatar da rasuwar mutanen, ya ce an garzaya da waɗanda suka samu raunuka zuwa Maiduguri
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Borno - Adadin mutanen da suka mutu sakamakon harin ƙunar baƙin wake da aka kai a yankin Gwoza da ke jihar Borno ya ƙaru zuwa mutum 18.
Hare-haren bam ɗin na ƙunar bakin waken dai ana zargin mata ne ƴan ƙungiyar ta'addan Boko Haram suka kaisu.
Borno: Mutum nawa suka rasu a harin bam?
Da farko dai rundunar ƴan sanda ta ce mutane shida ne suka mutu a hare-haren amma hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Borno (SEMA) ta tabbatar da mutuwar mutane 18, cewar rahoton jaridar Premium Times.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Darakta Janar na hukumar SEMA, Barkindo Saidu, ya bayyana cewa mutane 18 ne da suka haɗa da maza, mata da yara suka rasa rayukansu sakamakon hare-haren.
Channels tv ta ce ya ƙara da cewa harin farko da wata ƴar ƙunar bakin wake ta kai ya faru ne a wajen bikin aure, yayin da fashewar ta biyu ta faru ne a wajen jana’izar waɗanda suka mutu bayan wata ƴar ƙunar bakin wake ta shiga cikin jama’a.
"An garzaya da mutane 19 da suka samu munanan raunuka zuwa Maiduguri a cikin motocin ɗaukar marasa lafiya guda 4, yayin da wasu mutum 23 ke jiran rakiyar sojoji."
"Na kuma samu rahoton cewa an tayar da wani bam ɗin a Pulka."
- Barkindo Sa'idu
Ƙauyen Pulka dai ba shi da nisa da garin Gwoza.
An kai harin ƙunar baƙin wake a Borno
A wani labarin kuma, kun ji cewa aƙalla mutane shida ne suka rasa rayukansu bayan an harin ƙunar baƙin wake kan masu zaman makoki a jihar Borno.
Kwamishinan ƴan sandan jihar Borno, Yusuf Lawal wanda ya tabbtar da faruwar lamarin ya ce wata mace ce ta tayar da bam ɗin.
Asali: Legit.ng