IPMAN Ta Yi Zama Domin Rage Kudin Litar Mai, an Bayyana Sabon Farashin da Take Bukata

IPMAN Ta Yi Zama Domin Rage Kudin Litar Mai, an Bayyana Sabon Farashin da Take Bukata

  • Kungiyar dillalan mai ta IPMAN tana neman yadda za ta rage farashin litar mai zuwa N557 ganin yadda kullum man ke kara tsada
  • Kungiyar a jihohin Osun da Oyo ta yi wata ganawa ta musamman domin cimma matsaya kan yadda za a rage farashin
  • Hakan ya biyo bayan tsadar litar man a kasar sanadin cire tallafin mai da gwamnatin Bola Tinubu ta yi tun a watan Mayun 2023

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Kungiyar dillalan man fetur (IPMAN) ta yi wata ganawa domin duba yiwuwar rage farashin litar man.

Kungiyar da ke kula da jihohin Oyo da Osun ta yi ganawar a ranar Alhamis 27 ga watan Yunin 2024.

Kara karanta wannan

Yajin aiki: ASUU ta fadi matakin da ta dauka bayan ganawarta da gwamnatin tarayya

Kungiyar IPMAN ta yi wata ganawa domin rage farashin mai
Kungiyar IPMAN tana kokarin neman rage farashin man fetur bayan wata ganawa a jihar Oyo. Hoto: Getty Images.
Asali: Getty Images

IPMAN ta yi zama kan farashin mai

An gudanar da ganawar a sakatariyar IPMAN a Odo-Ona da ke kan babbar hanyar Ibadan zuwa Abeokuta, cewar Tribune.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahotannin sun tabbatar cewa a ganawar an bukaci rage farashin litar zuwa N557 daga N769 a wasu gidajen mai.

Sai dai kuma daga cikin wadanda suka halarci taron sun bukaci karin kudin litar mai din fiye da N1,000.

Duk da tattaunawa na tsawon lokaci ba a fitar da matsaya kan abin da aka gana da kuma sanin farashin ba.

Musabbabin tashin farashin mai a Najeriya

Mafi yawan gidajen mai suna siyar da litar man fetur N750 wasu har N770 yayin da wasu kuma kasa da haka.

Tashin farashin man ya faru ne tun bayan cire tallafin mai da gwamnatin Bola Tinubu ta yi a ranar 29 ga watan Mayun 2023.

Kara karanta wannan

An gano yadda fadar Shugaban kasa ta kashe N244m a sayen tayoyin mota a kwana 1

Daukar wannan mataki ya jefa al'ummar kasar cikin mawuyacin hali da tsadar kayayyaki musamman na abinci.

NNPCL ya musanta rage farashin mai

A wani labarin, kun ji cewa Kamfanin man fetur na Najeriya (NNPCL) ya ƙaryata rahotannin da ke yawo a soshiyal midiya cewa ya zabtare farashin fetur.

Babban jami'in yada labarai na kamfanin NNPC, Olufemi Soneye ya bayyana cewa rahoton sabon farashin fetur "ƙanzon kurege ne.

Soneye ta ce idan har an rage farashin mai din kamfanin man NNPCL shi zai fara fitar da sanarwa game da haka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.