Fulani Makiyaya Sun Yi Magana Kan Batun Tsige Sarkin Musulmi, Sun Yi Gargadi

Fulani Makiyaya Sun Yi Magana Kan Batun Tsige Sarkin Musulmi, Sun Yi Gargadi

  • Ƙungiyar makiyaya ta Miyetti Allah ta Najeriya (MACBAN) ta yi kira da a mutunta martaba da ƙimar kujerar Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar III
  • Shugaban ƙungiyar na ƙasa, Alhaji Baba Othman-Ngelzarma wanda ya yi wannan kiran ya ce bai kamata ƴan siyasa su riƙa yin wargi ga kujerar ba saboda muhimmanci da take da shi
  • Ya gargaɗi gwamnatin jihar Sokoto da ta yi taka tsan-tsan ta hanyar ƙin rage ƙarfin ikon da Sarkin Musulmin yake da shi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Ƙungiyar makiyaya ta Miyetti Allah ta Najeriya (MACBAN) ta jaddada buƙatar da ke akwai na kare kujerar Sarkin Musulmi.

Shugaban ƙungiyar ta MACBAN na ƙasa, Alhaji Baba Othman-Ngelzarma ne ya yi wannan kiran a wata sanarwa ranar Asabar a Abuja.

Kara karanta wannan

NLC: Bola Tinubu ya samu saƙon mafita kan mafi ƙarancin albashi a Najeriya

MACBAN ta bukaci a kare martabar kujerar Sarkin Musulmi
Kungiyar MACBAN ta bukaci a kare martabar kujerar Sarkin Musulmi Hoto: Daular Usmaniyya
Asali: Getty Images

Me MACBAN ta ce kan Sarkin Musulmi?

Ya ce bai kamata ƴan siyasa da ya kamata su yi amfani da ƙarfinsu wajen samar da shugabanci na gari ba ne za su riƙa yin wasa da kujerar Sarkin Musulmi wacce ta yi shekaru sama da 200, cewar rahoton jaridar The Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Alhaji Baba Othman-Ngelzarma ya soki barazanar rage ƙarfin ikon kujerar Sarkin Musulmi, wanda shi ne shugaban musulmai a Najeriya, rahoton Pulse.ng ya tabbatar.

"Mun yi amanna cewa kare martaba da ƙimar kujerar Sarkin Musulmi nauyi da ya rataya a wuyan duk wani mai hankali a ƙasar nan."
"Muna kira ga gwamnatin jihar Sokoto, musamman majalisa da su yi taka tsan-tsan tare da kare martabar kujerar saboda muhimmancin da take da shi."
"Mun damu matuƙa kan rahotannin da ke cewa gwamnatin jihar Sokoto na da niyyar rage ƙarfin ikon mai martaba Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar III."

Kara karanta wannan

An ba alkalai cin hanci a shari'ar zaben shugaban kasa na 2023? Gaskiya ta bayyana

- Alhaji Baba Othman-Ngelzarma

Batun tsige Sarkin Musulmi

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Sokoto ta musanta zargin da ƙungiyar MURIC ta yi na cewa tana shirin tsige mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III.

Ta kuma buƙaci mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima da ya rika bin diddigin gaskiya kafin ya yi tsokaci kan wasu muhimman batutuwan kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel