'Yan Bindiga Sun Kai Hari da Tsakar Dare, Sun Hallaka Bayin Allah da Dama
- Ƴan bindiga sun aikata ta'adi yayin da suka kai farmaki kauyen Ama Hausa da ke ƙaramar hukumar Okigwe a jihar Imo
- Bayanai sun nuna cewa maharan sun kashe mutum shida a harin wanda ya shafe tsawon sa'o'i gabanin sojoji su kai ɗauki
- Kwamishinan ƴan sandan jihar Imo, CP Ɗanjuma ya ce dakarun ƴan sanda ba za su huta ba sai sun tabbata sun cafke dukkan masu hannu a kisan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Imo - Ƴan bindiga sun kashe mutane shida a wani hari da suka kai kauyen Ama Hausa da ke karamar hukumar Okigwe a jihar Imo, kudu maso gabashin Najeriya.
Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun far wa al'ummar kauyen ba zato ba tsammani da tsakar daren ranar Laraba da ta gabata.
Lamarin ya faru ne sa'o'i kadan kafin wani hari na daban da aka kai ofishin 'yan sanda a karamar hukumar Ivo a jihar Ebonyi, kamar yadda Premium Times ta kawo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kamar dai a Ebonyi, ana zargin ‘yan bindigar da suka kai hari a jihar Imo ’yan kungiyar masu fafutukar kafa kasar Biafra ne (IPOB) da mayaƙansu ESN.
A yayin harin da aka kai yankin ƙaramar hukumr Okigwe, maharan sun ci karensu babu babbaka har zuwa karfe 9 na safiyar ranar Alhamis.
Wane mataki jami'an tsaro suka ɗauka?
A rahoton da jaridar Punch ta wallafa, sai bayan wayewar gari sannan jami'an rundunar sojojin Najeriya suka isa garin domin kai ɗauki.
Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Imo, Aboki Danjuma, ya sha alwashin cewa ‘yan sandan jihar za su zakulo wadanda suka yi kisan.
CP Danjuma ya faɗi hakan ne a lokacin da ya kai ziyara wurin da aka kai harin ranar Alhamis.
'Ina mai tabbatar muku da cewa rundunar ƴan sanda ba za ta yi ƙasa a guiwa har sai an kama wadanda suka aikata wannan aika-aika kuma an gurfanar da su a gaban kotu,” in ji shi.
Kwamishinan ya ce a halin yanzu ‘yan sanda tare da hadin gwiwar sojoji da ’yan banga sun bazama domin kakkabe ‘yan bindigar da ke da alhakin kisan.
Yan sanda sun mutu a harin Abia
Kuna da labarin Ƴan bindiga sun kai hari shingen binciken ababen hawa, sun kashe ƴan sanda biyu tare da jikkata wani a Aba da ke jihar Abia.
Lamarin dai ya tayar da hankulan mutanen da ke yankin waɗanda suka kulle shaguna suka koma gida gabanin a ƙara girke ƴan sanda a wurin.
Asali: Legit.ng