“Talauci Zai Ƙaru a Najeriya”: NLC Ta Gargaɗi Gwamnoni Kan Yanke Mafi Ƙarancin Albashi
- 'Yan ƙwadago sun soki gwamnoni kan bukatarsu na yanke sabon mafi ƙarancin albashi da kansu, abin da NLC ta kira 'mulkin mallaka'
- Kungiyar 'yan kwadagon ta ce idan har aka bar gwamnoni suka yanke albashi da kansu, to hakan zai jefa Najeriya cikin tsananin talauci
- NLC ta kuma yi gargadi ga gwamnoni kan cewa 'ba za su iya yanke abin da za a rika biyan ma'aikata ba' tare da aika sako ga Tinubu
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Kungiyar 'yan kwadago ta NLC ta ce ba ta gamsu da bukatar gwamnonin Najeriya ba na basu damar yanke mafi ƙarancin albashin jihohinsu da kansu.
NLC ta ce ba gwamnoni wuka da nama kan sabon mafi ƙarancin albashi tamkar ba kura ajiyar nama ne, kuma hakan zai kara jefa kasar a tsananin talauci.
NLC ta gargadi gwamnoni kan albashi
Kungiyar 'yan ƙwadagon ta ce bukatar gwamnonin tamkar nuna "mulkin mallaka" ne wanda ba zai yi tasiri a wajen zartar da mafi ƙarancin albashi ba, in ji rahoton The Nation.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
NLC ta nemi Shugaba Bola Tinubu da ta guji bude kofar da gwamnoni za su iya cika shi da kalaman yaudara kan lamarin, la'akari da alkawarin da ya daukarwa ma'aikata.
Shugaban sashen yaɗa labarai da hulda da jama'a na NLC, Benson Upah ya bayyana hakan a wata sanarwa mai taken 'gwamnoni ba za su iya yanke abin da za a biya mu ba.'
NLC ta faɗi illar yanke albashi a jihohi
Jaridar Premium Times ta ruwaito Mista Upah ya yi nuni da cewa bukatar gwamnonin na yanke sabon albashin da kansu barazana ce ga ma'aikata da kuma tattalin arzikin kasa.
Ya jaddada cewa makomar ma'aikatan Najeriya ba za ta taɓa zama a hannun masu ɗaukar aiki ba, walau na gwamnati ko kamfanoni masu zaman kansu.
Kakakin NLC ya kuma ce idan har gwamnoni suka samu abin da suke so, to hakan zai sa kamfanoni su rika biyan ma'aikatansu albashin da duk suka ga dama.
Gwamnoni sun nemi yanke sabon albashi
Tun da fari, mun ruwaito cewa kungiyar gwamnonin Kudu ta nemi Shugaba Bola Tinubu da ya amincewa gwamnoni su biya sabon mafi ƙarancin albashi gwargwadon karfinsu.
Gwamnoni 17 da ke a karkashin kungiyar sun ce a kyale jihohi su tattauna da 'yan kwadago da ke a jihohinsu domin cimma matsaya kan sabon albashin da za su rika biyansu.
Asali: Legit.ng