Gwamnatin Jigawa Ta Fara Shirin Sayen Jami'ar Kuɗi, Ta Kafa Kwamitoci 3
- Gwamna Umar Namadi ya amince da rahoton kwamitin majalisar zartarwa na sayen Jami'ar Khadija ta dawo hannun gwamnatinsa
- Fitacciyar jami'ar ta kudi ta shiga matsaloli da dama ciki har da karayar arziki wanda ya sa masu ita suka yi tayin sayar da ita ga gwamnatin Jigawa
- A halin yanzun gwamnatin Ɗanmodi ta kafa kwamitoci uku da za su ba ta shawara kan saye da gyara jami'ar
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Jigawa - Gwamnatin jihar Jigawa ta fara shirye-shiryen sayen jami'ar Kahadijah da ke Majia domin inganta harkokin ilimi a jihar.
Hakan ya biyo bayan amincewar Gwamna Umar Namadi da rahoton kwamitin majalisar zartaswa na tayin sayen jami'ar domin ta dawo hannun gwamnati.
Attajirin ɗan kasuwa mai taimakon jama'a, Alhaji Abdulaziz Garba Namadi ne ya kafa jami'ar a 2014 a matsayin makarantar kuɗi domin samar da ilimi mai nagarta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, gwamnatin Jigawa ta karɓi tayin da aka mata na sayen jami'r a wani ɓangare na ƙoƙarin faɗaɗa hanyoyin neman ilimi ga al'umma.
Meyasa za a sayar da jami'ar Khadijah?
Jami'ar, wacce aka sanya wa sunan mahaifiyar wanda ya kafa ta, Khadija, ta zama babbar jami'a a yankin kuma tana koyar da kwasa-kwasai a fannin ilimi, kasuwanci da kimiyya.
To amma saboda karayar arziki da wau ƙalubale, jami'ar ta gaza zama da kafafunta wanda ya sa mahukuntan makarantar suka fara tunanin sayar da ita ga gwamnati.
Gwamnatin Jigawa ta amince da tayin
Bayan duba kimar jami'ar da kuma gudummuwar da take bayarwa a harkar ilimi a Jigawa, gwamnatin Ɗanmodi ta kafa kwamitoci na musamman guda uku.
Waɗannan kwamitoci za su yi aiki ne domin bai wa gwamnatin jihar shawara kan matakan sayen jami'ar da kuma yadda za a gyarata idan haƙar ta cimma ruwa.
Kwamitocin, wadanda suka kunshi kwararru a fannin ilimi, kudi da doka, za su tantance gine-gine da albarkatun jami’ar da kuma harkokin gudanarwa.
Jigawa za ta zauna kan ƙarin albashi
Kun ji cewa Gwamna Umar Namadi na jihar Jigawa ya ce har yanzu gwamnatin jihar ba ta yanke adadin da zata biya a mataayin sabon mafi karancin albashi ba.
Namadi ya bayyana cewa gwamnatin Jigawa ba ta ma fara tattaunawa kan ƙarin albashi da ƙungiyar kwadago ta jihar ba.
Asali: Legit.ng