Kano: Ana Fargabar Mutane Sun Mutu Yayin da Gini Ya Rufta Kansu Ana Ruwan Sama
- Wani gini da ake kan aiki a Kuntau da ke cikin kwaryar birnin Kano ya rufta kan ma'aikata da wasu mutane ranar Jumu'a
- Rahotanni sun bayyana cewa ginin ya danne mutane 5 ciki hada mai gidan kuma ana fargabar takwas daga ciki sun rasu
- Binciken farko da aka gudanar kan musabbabin faruwar lamarin ya nuna cewa ginin ya rufta ne sakamakon amfani da kayan aiki mara inganci
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano - Ana fargabar akalla mutane takwas sun mutu a lokacin da wani gini mai hawa daya ya rufta a unguwar Kuntau da ke karamar hukumar Gwale a jihar Kano.
Lamarin dai ya faru ne da sanyin safiyar Juma’a, 28 ga watan Yuni, 2024 yayin da ma’aikata ke ci gaba da aikin ginin ana tsaka da ruwan sama.
Majiyoyi daga yankin sun bayyana cewa ginin ya danne akalla mutane 15 ciki har da mai ginin, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An tattaro cewa mai wurin wanda ake kira da Sharu a taƙaice, yana gina wurin ne domin haɗe shi da gidansa da yake ciki.
Gini ya rufta ana ruwan sama a Kano
Haka nan kuma an gano cewa wasu daga cikin mutanen da ginin ya danne sun zo wucewa ne amma sakamakon ruwan sama suka shiga karkashin ginin don su fake.
Faruwar lamarin ke da wuya, matar Sharu ta fito da gudu tana kukan neman taimako.
Nan take makwabta da masu wucewa suka yi gangami domin ceto wadanda suka makale a karkashin baraguzan ginin.
An bayyana cewa tuni aka garzaya da mutane bakwai zuwa asibitin kwararru na Murtala Muhammad amma mutum daya ya mutu tun a hanya.
Mutum nawa suka rasu?
Wani ma’aikacin hukumar kashe gobara ta Kano da ya nemi a sakaya sunansa, ya tabbatar da cewa ginin ya danne mutane 15 kuma zuwa yanzu mutum bakwai sun mutu.
Sai wajen karfe 7:30 na dare sannan motocin hukumar kashe gobara da jami’an ‘yan sanda suka bar unguwar domin tabbatar da cewa babu wanda ya makale a ginin.
Rahoton binciken farko da aka yi ya nuna cewa ginin ya rufta ne sakamakon amfani da kayan gini marasa inganci.
Tirela ta bi kan masallata a Kano
A wani rahoton kun ji cewa an shiga wani irin yanayi bayan wasu masallata sun rasa ransu suna tsaka da sallah a masallacin Juma'a bayan tirela ta hau kansu.
Lamarin ya faru ne a garin Imawa da ke karamar hukumar Kura a jihar Kano a yau Juma'a 28 ga watan Yunin 2024.
Asali: Legit.ng