Shugaban Kasa Bola Tinubu Ya Amince da Nadin Manyan Mukamai 8 a Gwamnatin Tarayya

Shugaban Kasa Bola Tinubu Ya Amince da Nadin Manyan Mukamai 8 a Gwamnatin Tarayya

  • Folashade Yemi Esan ta zakulo wadanda za su zama manyan sakatarori a ma’aikatun gwamnatin tarayya da ke Abuja
  • Shugaban ma’aikatan gwamnatin tarayyar ta gabatar da sunayen jami’ai takwas wadanda Bola Tinubu ya yi na’am da su
  • Cif Ajuri Ngalale ya sanar da haka a matsayinsa na mai taimakawa shugaban kasa wajen harkokin sadarwa da yada labarai

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya nada manyan sakatarori a gwamnatin tarayya kamar yadda rahoto ya fito daga fadar shugaban Najeriya.

Mai girma Bola Tinubu ya amince da nadin wadannan sakatarori ne bayan gibin da aka samu a sakamakon ritayar wasu daga bakin aiki.

Tinubu
Shugaban kasa Bola Tinubu ya yi nadin mukamai Hoto: Hoto: www.bisiakande.com
Asali: UGC

Gidan talabijin NTA ya bayyana cewa nadin ya ratsa daukacin bangarorin da ake da su a kasar nan.

Kara karanta wannan

Jihohi 3 da ke zargin gwamnatin tarayya da yi masu katsalandan

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bola Tinubu ya yi nadin mukamai

An dauko wadanda aka ba mukaman ne daga jihohin Bauchi, Zamfara da Jigawa a Arewa maso yamma da kuma yankin Arewa maso gabas.

Akwai wadanda aka nada daga Akwa Ibom a Kudu maso kudu da Anambra a Kudu maso gabas sai wani daga Ondo a kudu maso yamma.

Ajuri Ngalale wanda ya sanar da nadin mukaman ya tabbatar da cewa bangaren kudu maso gabas da kudu maso kudu sun samu karin kujeru.

Mai Magana da yawun shugaban kasar ya ce an zakulo su ne bayan an bi ka’idar aikin gwamnati, The Guardian ta fitar da labarin nan.

Mai alhakin wannan aiki ita ce shugabar ma’aikatar gwamnatin tarayya, Folashade Yemi Esan wanda ta ke shirin yin ritaya a shekarar nan.

Su wanene Tinubu ya nada a mukaman?

Kara karanta wannan

Ruwa ya cinye wasu dalibai a hanyarsu ta dawo wa daga jarrabawa a Kaduna

1. Dr. Emanso Umobong Okop - Akwa-Ibom

2. Obi Emeka Vitalis - Anambra

3. Mahmood Fatima Sugra Tabi'a - Bauchi

4. Danjuma Mohammed Sanusi - Jigawa

5. Olusanya Olubunmi - Ondo

6. Dr. Keshinro Maryam Ismaila - Zamfara

7. Akujobi Chinyere Ijeoma (Kudu maso gabas)

8. Isokpunwu Christopher Osaruwanmwen (Kudu maso kudu)

A karshen sanarwar, Ajuri Ngelale ya ce Bola Tinubu yana fatan wadanda aka ba mukaman za su yi aikinsu yadda al’ummar kasar suke bukata.

An bukaci su na jajircewa, amana da kishin kasa a kujerunsu na manyan sakatarorin gwamnati.

Shettima ya ce ayi hakuri da Tinubu

A rahoton da aka fitar a baya, an ji cewa Kashim Shettima ya sake rokon ƴan Najeriya su cigaba da hakuri da mulkin shugaba Bola Tinubu.

Shettima ya bukaci ƴan kasa su yiwa Tinubu adalci wurin kimanta gwamnatinsa, ya ce matsalar tattalin arziki ta zama ruwan dare.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel