Katsina: An Kama Mutum 2 da Hannu a Sace Mahaifiyar Dauda Kahutu Rarara

Katsina: An Kama Mutum 2 da Hannu a Sace Mahaifiyar Dauda Kahutu Rarara

  • Ƴan sanda sun kama wasu mutum biyu bisa zarginsu da hannu a garkuwa da mahaifiyar fitaccen mawakin siyasa, Dauda Kahutu Rarara
  • Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ƴan sandan Katsina, ASP Abubakar Sadiq ya ce yanzu haka suna kan bincike don ceto dattijuwar
  • Wasu ƴan bindiga sun shiga gidan Rarara da ke mahaifarsa Kahutu a ƙaramar hukumar Ɗanja, suka tafi da mahaifiyarsa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Katsina - Rundunar ƴan sanda ta cafke mutum biyu da ake zargin suna da hannu a sace mahaifiyar fitaccen mawakin siyasa, Dauda Adamu Kahutu Rarara.

Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ƴan sandan jihar Katsina, ASP Abubakar Sadiq Aliyu ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar yau Jumu'a.

Kara karanta wannan

Zamfara: 'Yan bindiga 100 sun kai hari kan bayin Allah, sun tafka mummunar ɓarna

Dauda Kahutu Rarara.
'Yan sanda sun kama mutum 2 da zargin suna da hannu a sace mahaifiyar Rarara Hoto: Dauda Kahutu Rarara
Asali: Facebook

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, ASP Abubakar ya ce yanzu haka waɗanda ake zargin suna hannun jami'ai ana ci gaba da bincike a kansu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴan sanda sun kama mutum 2

"Ofishin ƴan sanda na Ɗanja ya samu rahoton cewa masu garkuwa sun shiga gidan Hajiya Halima Adamu da ke garin Kahutu da misalin ƙarfe 1:30 na daren yau Jumu'a, suka tafi da ita.
"Nan take jami'an ƴan sanda suka nufi wurin da lamarin ya faru da niyyar kama masu hannu a harin gami da ceto matar cikin ƙoshin lafiya.
"A binciken da suka yi ne ƴan sandan suka kama mutum biyu da ake zargi, a halin yanzu muna kan aiki za mu sake fitar da bayanai a lokacin daya dace."

- ASP Abubakar Sadiq Aliyu.

Rarara dai ya shahara a fagen waƙe-waƙen siyasa kuma ya taka rawa wajen tallata takarar shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu musamman a garuruwan Hausawa.

Kara karanta wannan

Katsina: Ƴan bindiga sun yi garkuwa da mahaifiyar fitaccen mawakin siyasa Rarara

Dauda Kahutu ya riƙe muƙamin shugabam mawakan shugaban ƙasa a lokacin muƙkin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.

Wane matakin gwamnatin Katsina ta ɗauka?

A halin yanzu kwamishinan tsaro na jihar Katsina, Nasiru Mu'azu ya ce ƴan bindiga sun bi ta bayan gida ba tare da kowa ya sani ba, sun sace mahaifiyar Rarara a Kahutu

A rahoton Leadership, ya ce tuni aka tura ƙarin jami'an tsaro domin su bi sawun maharan da nufin ceto dattijuwar.

Ƴan bindiga sun sace mutane a Zamfara

Kun ji cewa Yan bindiga sun kai hari kauyen Danbaza da ke ƙaramar hukumar Maradun a jihar Zamfara, sun yi awon gaba da mutane 47.

Mazauna garin sun bayyana cewa ƴan bindigar kusan su 100 ɗauke da makamai, sun buɗe wuta yayin da suka kewaye garin da tsakar dare.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel