Zamfara: Yan Bindiga 100 Sun Kai hari Kan Bayin Allah, Sun Tafka Mummunar Ɓarna
- Yan bindiga sun kai hari kauyen Danbaza da ke ƙaramar hukumar Maradun a jihar Zamfara, sun yi awon gaba da mutane 47
- Mazauna garin sun bayyana cewa ƴan bindigar kusan su 100 ɗauke da makamai, sun buɗe wuta yayin da suka kewaye garin da tsakar dare
- Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ƴan sandan jihar Zamfara, ASP Yazid Abubakar ya tabbatar da faruwar harin
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Zamfara - ‘Yan bindiga sun kai hari tare da yin garkuwa da mutane 47 daga kauyen Danbaza a karamar hukumar Maradun ta jihar Zamfara.
Wani mazaunin ƙauyen, Abdul Danbaza, ya bayyana cewa ƴan bindigar sun mamaye garin da misalin ƙarfe 2:30 na dare ranar Laraba.
Ya shaidawa jaridar Leadership cewa maharan sun yi awon gaba da mutane 47 galibi mata da ƙananan yara zuwa cikin jeji.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Zamfara: Ƴan bindiga sun sace mutum 47
Abdul ya ce ƴan bindigar, waɗanda adadinsu ya kai 100 duka a kan babura ɗauke da mugayen makamai sun buɗe wuta daga shiga kauyen.
Mutumin ya kara da cewa shi kansa yana cikin waɗanda maharan suka tattara suka tasa zuwa jeji amma a hanya ya samu ya ɓuya a bayan wata itaciya, ya dawo gida.
"Na taki sa’a da na kubuta daga hannun ‘yan fashin dajin da suka kai farmaki kauyenmu, amma abin takaici, mahaifina da wasu iyalina suna cikin waɗanda aka yi garkuwa da su.
Hali da mutane ke ciki a Maradun
A ƴan kwanakin nan ƴan bindiga sun yiwa mutane barazanar kai hari a kauyuka daban-daban da ke ƙarƙashin ƙaramar hukumar Maradun a jihar Zamfara.
Kauyukan da ƴan bindiga suka kai hare-hare kwanan nan a ƙaramar hukumar Maradun sun haɗa da Janbako, Gora Namaye, Kaya, da cikin garin Maradun.
Maradun dai nan ne mahaifar karamin ministan tsaro kuma tsohon gwamnan Zamfara, Muhammad Bello Matawalle.
Yan sanda sun tabbatar da harin
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara, ASP Yazid Abubakar, ya tabbatar da harin da aka kai kauyen Danbaza kuma ya yi alkawarin sakin bayanai nan gaba, Daily Post ta rahoto.
An sace mahaifiyar Rarara
A wani rahoton kuma ƴan bindiga sun kai farmaki gidan fitaccen mawakin siyasa, Dauda Adamu Rarara, sun yi awon gaba da mahaifiyarsa a jihar Katsina.
Legit Hausa ta tattaro cewa maharan sun kutsa sabon gidan Rarara da ke gabashin Kahutu a ƙaramar hukumar Ɗanja jiya da daddare.
Asali: Legit.ng