Sojoji Sun Ragargaji Yan Bindiga a Sokoto, Sun Ceto Mutanen da Aka Cafke

Sojoji Sun Ragargaji Yan Bindiga a Sokoto, Sun Ceto Mutanen da Aka Cafke

  • Rundunar sojin Najeriya ta samu nasara kan yan bindiga bayan sun fafata a wani kazamin fada a jihar Sokoto dake Arewa maso yamma
  • An fafata tsakanin sojojin Najeriya da yan bindiga ne a ƙauyukan Baniguntu da Gohonau da ke karamar hukumar Gudu a jihar ta Sokoto
  • Rundunar sojin ta bayyana adadin mutanen da ta ceto a hannun yan bindigar da kayan fada da ta kwato a wajensu bayan sun fafata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Sokoto - Rundunar sojin Najeriya ta fafata da yan bindiga a wasu ƙauyukan jihar Sokoto a jiya Alhamis.

Rundunar sojin ta samu nasarar kashe wasu daga cikin yan bindigar da kwato makamai masu yawa.

Kara karanta wannan

Kaduna: Rundunar sojojin Najeriya ta samar da hanyar magance rashin tsaro

Sojojin Najeriya
Sojojin Najeriya sun kashe 'yan ta'adda a Sokoto. Hoto: HQ Nigerian Army
Asali: Facebook

Legit ta gano haka ne cikin wani sako da rundunar sojin Najeriya ta wallafa a shafinta na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda sojoji suka fafata a Sokoto

A jiya Alhamis ne sojojin Najeriya suka samu kiran gaggawa yayin da yan bindiga ke ƙoƙarin garkuwa da mutane a karamar hukumar Gudu.

Sojin sun afkawa yan bindigar kuma sun yi musayar wuta wanda hakan ya jawo kashe yan bindiga biyar sauran kuma suka tsere da munanan raunuka.

Abubuwa da sojoji suka kwato

Rundunar sojin Najeriya ta yi nasarar ceto mutane biyu da yan bindigar suka yi garkuwa dasu yayin artabun.

Haka zalika rundunar sojin ta kwato makamai masu yawa ciki har da bindigogi ƙirar AK47 guda biyar.

Har ila yau sojojin sun kwato harsashi masu yawa da wayar hannu kirar Techno da kuma lalata sansanin yan bindigar.

Rundunar sojin ta ce za ta cigaba da ƙoƙarin farautar yan ta'adda a sassan Najeriya domin tabbatar da zaman lafiya.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi yunƙurin takaita babban limamin Musulmi a jihar Kaduna

Sojojin sun fadi nasarar da suka samu

A wani rahoton, kun ji cewa hedkwatar tsaro ta ƙasa (DHQ) ta bayyana nasarorin da dakarun sojojin Najeriya suka samu a yaƙin da suke yi da ƴan ta'adda a ƙasar nan.

Hedkwatar tsaro ta ƙasa ta bayyana cewa daga watan Afirilu zuwa watan Yunin shekarar 2024, dakarun sojoji sun hallaka ƴan ta'adda 2,245.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Online view pixel