Gwamnatin Sokoto Ta Fadi Abin da Zai Hana Dawo da Hakiman da Aka Tsige Duk da Umurnin Kotu

Gwamnatin Sokoto Ta Fadi Abin da Zai Hana Dawo da Hakiman da Aka Tsige Duk da Umurnin Kotu

  • Gwamnatin jihar Sokoto ta bayyana abin da doka ta ce bayan hakimai da aka tsige suka kai kara kotu domin a mayar dasu kujerunsu
  • Kwamishinan shari'a na jihar Sokoto, Barista Nasiru Binji ne ya yi karin haske yayin da al'amarin ke cigaba da jan hankulan al'umma
  • Tun asali dai gwamnatin jihar ta tsige hakimai 15 bisa zargin su da laifuffuka inda wasunsu suka shigar da gwamnatin kara gaban kotu

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Sokoto - Gwamantin jihar Sokoto ta yi karin haske kan hukuncin da kotu ta yi na hana tsige wasu hakimai.

Hakan na zuwa ne bayan wasu hakimai cikin 15 da gwamnatin ta tsige sun shigar da kara gaban alkali domin neman hakkinsu.

Kara karanta wannan

Rikicin sarauta: Kotu ta haramtawa gwamnatin Sokoto tsige hakimai

Sokoto
Gwamnatin Sokoto ta yi karin haske kan tsige hakimai. Hoto: Ahmed Aliyu Sokoto.
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa kwamishinan shari'a na jihar, Barista Nasiru Binji ne ya yi karin hasken.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsige hakimai: Kotu ta makara inji kwamishina

Kwamishinan shari'a na jihar Sokoto, Barista Nasiru Binji ya ce umurnin da kotu ta bayar na dakatar da sauke hakimai ya zo a makare.

Barista Nasiru Binji ya tabbatar da cewa kotun ta bayar da umurnin ne bayan lokaci da doka ta ba ta dama ya wuce, rahoton 21st Century Chronicle.

Saboda haka kwamishinan ya ce a halin yanzu hakiman da aka tsige ba su da wata madogara na iƙirarin cewa a dawo dasu.

Tsige hakimai: Abin da doka ta ce

Kwamishinan shari'a na jihar Sokoto ya ce doka ta bada damar a dakatar da tsige hakimai ne kwana 7 idan aka samu umurnin kotu.

Barista Binji ya kuma tabbatar da cewa an tsige hakiman ne a ranar 13 ga wata wanda daga ranar 20 ga wata basu da wata mafaka a idon doka.

Kara karanta wannan

Kotu ta yanke hukunci kan Emefiele, an gano miliyoyin daloli da aka wawushe

Rahotanni sun nuna cewa a ranar 23 ga watan Yuni ne aka saurari karar hakiman da aka tsige a gaban kotu wanda ya nuna sun makara da kwana uku.

MURIC ta yi magana kan tsige Sultan

A wani rahoton, kun ji cewa Kungiyar kare hakkin Musulmi (MURIC) ta sake magana kan zargin yunkurin da gwamnatin Sokoto ke yi na tsige Sultan.

Shugaban MURIC, Farfesa Ishaq Lakin Akintola ya bayyana yadda tsige Sultan zai shafi dukkan al'ummar Musulmi a fadin Najeriya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Online view pixel