Lauyoyin Yahaya Bello Sun Shiga Uku, Hukumar EFCC Ta Roƙi Kotu Ta Ɗaure Su

Lauyoyin Yahaya Bello Sun Shiga Uku, Hukumar EFCC Ta Roƙi Kotu Ta Ɗaure Su

  • Tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello ya jefa lauyoyin da ke kare shi a matsala bayan gaza gurfana da ya yi gaban babbar kotu a Abuja
  • An ruwaito cewa hukumar EFCC ta nemi kotu ta ba da izini a tasa keyar lauyoyin Yahaya Bello gabanta saboda sun ƙarya dokar gudanar da aiki
  • An ce sau da dama lauyoyin tsohon gwamnan sun sha daukar alkawarin gurfanar da shi gaban kotu amma har yanzu basu cika alkawarin ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Hukumar EFCC ta nemi babbar kotun tarayya da ke Abuja da ta ɗaure wasu manyan lauyoyi biyu, Ifedayo Adedipe da Abdulwahab Muhammed kan zargin ɓata aiki.

Kara karanta wannan

Lauyan da ke kare Yahaya Bello ya watsa masa kasa a ido ana cikin zaman kotu

EFCC ta shaidawa kotun cewa manyan lauyoyin sun gaza gabatar da Yahaya Bello gaban kotu wanda hukumar ke zargi da almundahanar N80.2bn.

EFCC ta yi magana kan lauyoyin da ke kare Yahaya Bello
EFCC ta nemi kotu ta ladabtar da lauyoyin da ke kare Yahaya Bello. Hoto: @officialEFCC, @OfficialGYBKogi
Asali: Facebook

"A tuhumi lauyoyin Yahaya Bello" - EFCC

Kamar yadda hukumar ta wallafa a shafinta na intanet, ana tuhumar Yahaya Bello tare da ɗan uwansa Ali Bello, Dauda Suleiman da Abdulsalam Hudu kan laifuffuka 19.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A zaman kotun na ranar Alhamis, lauyan EFCC, Kemi Pinhero (SAN) ya roki kotun da ta ladabtar da Abdulwahab da Adeola saboda gaza cika alkawarin gurfanar da tsohon gwamnan.

Kemi Pinhero SAN ya ce:

"Ina rokon wannan kotu mai alfarma da ta gurfanar da lauyoyin saboda sun ɓata aiki, akwai buƙatar su fuskanci hukunci, musamman tun da Adedipe yana nan, a fara ta kansa.
"Doka ta 32, sakin layi na 33 na kundin dokokin aikinmu na 2023, ya ce duk lauyan da ya gaza cika alkawarin da ya dauka a madadin kasan ko wanda yake wakilta ya saɓa doka."

Kara karanta wannan

Kotu ta tasa keyar 'Sanata' zuwa kurkuku saboda zargin damfarar 'yar kasar waje

Lauyoyi sun gaza gurfanar da Yahaya Bello

Sau tari Mohammed da Adedipe sun sha daukar alkawarin za su gurfanar da tsohon gwamnan na Kogi a gaban kotu, amma sun gaza cika alkawarin.

A zaman kotun na ranar Alhamis muka ruwaito Adedipe ya shaidawa kotun cewa sun mika buƙata ga babban alkalin babbar kotun tarayya na a mayar da shari'ar zuwa jihar Kogi.

Sai dai lauyan EFCC ya dage kan cewa abin da ya tara su a kotu a ranar shi ne sanin dalilin da ya sa lauyoyin suka gaza gurfanar da Yahaya Bello duk da alkawarin da suka dauka.

A karshe dai Mai shari'a Emeka Nwite ya dage shari'ar zuwa ranar 17 ga watan Yuli idan zai duba bukatar da aka gabatar na gurfanar da lauyoyin Yahaya Bello.

Lauyan Yahaya Bello na son zame kansa

A wani labarin, mun ruwaito cewa Adeola Adedipe (SAN), daya daga cikin lauyoyin da ke kare Yahaya Bello ya mika takardar janyewa daga kare tsohon gwamnan Kogi.

Kara karanta wannan

Emefiele: Bayan ƙwace kadarorin N12bn, tsohon gwamnan CBN ya nemi alfarma a kotu

Adedipe ya ce ba zai iya ci gaba da kare Yahaya Bello a shari'arsa da hukumar EFCC ba, abin da lauyan hukumar ya ki amince da shi inda ya ce bakin alkalami ya bushewa Adedipe.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel