Zamfara: Malamin Addinin da Ƴan Bindiga Suka Yi Garkuwa da Shi Ya Turo Saƙo

Zamfara: Malamin Addinin da Ƴan Bindiga Suka Yi Garkuwa da Shi Ya Turo Saƙo

  • Malamin cocin da ƴan bindiga suka yi garkuwa da shi a jihar Zamfara ya turo saƙo mai ɗaga hankali kan halin da yake ciki
  • Mikah Suleiman na cocin St. Raymond ya roƙi al'umma da gwamnati su taimaka su karɓo shi daga hannun ƴan fashin daji
  • Ya bayyana haɗarin da yake ciki saboda ƴan fashin sun gaya masa ba za su ci gaba da tsare shi ba matuƙar ba a biya fansa ba

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Zamfara - Mikah Suleiman, limamin cocin St. Raymond Catholic Church wanda ƴan bindiga suka yi garkuwa da shi a Damba, Gusau, jihar Zamfara, ya turo saƙo.

Malamin cocin ya roƙi mutane da gwamnati su dubi girman Allah su taimaka a kubutar da shi daga hannun masu garkuwa.

Kara karanta wannan

Gwamnoni 36 sun gana a Abuja, sun cimma matsaya kan sabon mafi ƙarancin albashi

Mikah Suleiman.
Limamin coci da yan bindiga suka sace a Zamfara yana neman taimako Hoto: @SGebells
Asali: Twitter

Fasto a hannun 'yan bindiga a jeji

A wani faifan bidiyo mai tsawon dakika 51 da ya bazu a shafukan sada zumunta, an hangi Suleiman sanye da shudiyar riga da gajeren wando, yana zaune a kasa yayin da yake neman taimako.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

The Cable ta tattaro cewa ‘yan bindiga sun sace Suleiman ne da safiyar ranar 22 ga watan Yuni a cikin harabar cocin da ke Gusau, babban birnin jihar Zamfara.

Malamin cocin ya turo saƙo

Limamin cocin ya ce shi kadai ne ya rage ‘yan fashin dajin ke tsare da shi a halin yanzu.

"Ina rokon a taimaka a 'yantar da ni daga wannan wuri, sun gaya mini cewa ba su ajiye mutane a nan na dogon lokaci. Duk wanda suka ɗauko ba ya wuce mako guda."
“Sun gaya mani cewa kashe mutum ba wani abu ba ne a wurinsu, sannan suna tsare da ni saboda su taimake ni. Don Allah ku cece ni, ku ceto rayuwata, ku dubi kaina da kafafuna a ɗaure nake."

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi yunƙurin takaita babban limamin Musulmi a jihar Kaduna

"Sun saba idan suka sato mutum ba su ɓata loƙaci, idan ƴan uwansa suka gaza biyan kuɗin fansa nan take suke kashe shi. Don girman Allah ku kawo mun agaji."

Ƴan daƙiƙu kadan gabannin karewar bidiyon, an ga ɗaya daga cikin ƴan fashin ya sa sanda yana shafa kansa, kamar yadda Daily Post ta ruwaito.

Zamfara: Ƴan bindiga sun kai hari Masallaci

Kun ji cewa ƴan bindiga sun kai hari masallaci a lokacin da mutane ke shirin Sallar Asuba a kauyen Tazame da ke ƙaramar hukumar Bungudu a Zamfara.

Rahotanni sun nuna cewa ƴan bindigar sun kashe ladani da ƙaninsa, sun yi awon gaba da mutane da dama yau Talata da safe.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel