Rikicin Siyasa: Gwamna da Magoya Bayansa Sun Dawo Daga Rakiyar Jam’iyyar PDP

Rikicin Siyasa: Gwamna da Magoya Bayansa Sun Dawo Daga Rakiyar Jam’iyyar PDP

  • Gwamna Siminalayi Fubara ya bayyana rashin jin dadinsa ga jam'iyyar PDP inda ya ce ta gaza a jihar Rivers
  • Gwamna Fubara ya bayyana cewa jam'iyyar ta gaza wajen cimma muradunsa da magoya bayansa a jihar
  • Fubara ya kuma yi tsokaci kan rikicin da yaƙi ci yaƙi cinye wa a jihar, ciki har da wani yunkuri na dasa bam

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Port-Hacourt, Rivers - Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Rivers ya bayyana rashin jin dadinsa game da jam'iyyar PDP.

Gwamna Simi Fubara ya ce PDP ta gaza wajen cimma muradunsa da na magoya bayansa a jihar Rivers, wanda ya sa kowa ya ke dawowa daga rakiyarta.

Kara karanta wannan

Ruwa ya cinye wasu dalibai a hanyarsu ta dawo wa daga jarrabawa a Kaduna

Fubara ya yi magana kan jam'iyyar PDP a Rivers
Gwamna Fubara ya ce jam'iyyar PDP ta gaza a jihar Rivers. Hoto: @SimFubaraKSC, @GovWike
Asali: Facebook

Gwamna Fubara ya ce jam'iyyar PDP ta gaza

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa gwamnan jihar na Rivers ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, yayin ganawa da kwamitin majalisar dattawa kan kasuwanci a garin Fatakwal.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Fubara dai ya zama gwamnan Rivers ne karkashin PDP, amma ya ce ba zai yi biyayya ga tsare-tsaren jam'iyyar ba saboda sun kunyata jama'a da yawa.

Gwamnan ya ce shi da magoya bayan shi yanzu sun koma tafiya ne a matsayin kungiya da ke rajin kare dimokuraɗiyya ba wai a matsayin jam'iyyar siyasa ba, inji rahoton Daily Trust.

Fubara ya magantu kan yunkurin dasa bam

Har ila yau, Gwamna Fubara ya magantu kan wani rikici da ya mamaye jihar biyo bayan yunkurin dasa bam da aka yi a wani otel da ke Fatakwal a ranar Talata, 25 ga Yuni.

Kara karanta wannan

Mutuwar jami’in Kwastam: Shugaba Tinubu ya aikawa Iiyalin Marigayi Etop Essien saƙo

Vanguard ta ruwaito cewa wasu bata gari ne suka yi yunkurin tayar da bam a otel din wanda manyan mutane ke sauka ciki har da mambobin majalisar dattawa.

An ruwaito cewa yan sanda sun samu nasarar kama wanda ake zargi da ta'adin.

Gwamna Fubara ya ce wannan yunkurin ya alamta muhimmancin aiwatar da dokar ta ɓaci a jihar Rivers kamar yadda wasu suke buri.

APC ta soki Fubara kan kaddamar da ayyuka

A wani labarin, mun ruwaito cewa, jam'iyyar APC ta ce gwamnan jihar Rivers ya kaddamar da wasu ayyuka da Nysome Wike ya yi a matsayin nasa.

APC ta ce ayyukan da Fubara ya kaddamar a lokacin bikin cikarsa shekara daya ba nasa ba ne don haka bai kamata ya rika tutiya da aikin da tsohon gwamnan jihar ya yi ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel