Majalisar Dattawa Ta Yiwa Tinubu Gata, an Tsawaita Wa’adin Aiwatar da Kasafin 2023
- Majalisar dattawa ta amince da wata bukata da shugaban kasa Bola Tinubu ya gabatar mata kan kasafin kudin 2023 da ƙarin kasafin shekarar
- Shugaba Tinubu ya roki majalisar ta tsawaita wa'adin amincewa da kudurorin dokar kasafin kudin 2023 saboda aiwatar da wasu ayyuka
- Majalisar ta bayyana cewa tsawaita wa'adin zai kare ne a ranar 30 ga Disambar 2023 kuma dokar za ta yi aiki tare da kasafin 2024
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Majalisar dattawa ta 10 ta kafa tarihi a ranar Alhamis, 27 ga watan Yuni bayan ta yarda ta tsawaita wa'adin amincewa da kudurin dokar kasafin kudin 2023.
Haka zalika, a zaman majalisar na yau, sanatocin sun yarda za a tsawaita wa'adin amincewa da kudirin dokar ƙarin kasafin kudin 2023 har zuwa ranar 31 ga watan Disambar 2024.
Tinubu ya aika wasika ga majalisar dattawa
Wannan matsayar na nufin cewa kudirorin dokar kasafin kudin 2023 da ƙarin kasafin za su ci gaba da aiki tare da kudurin dokar kasafin kudin 2024, in ji rahoton The Nation.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Majalisar dattawan ta cimma wannan matsayar ne bayan da Shugaba Bola Tinubu ya gabatar mata da buƙatar tsawaita wa'adin cikin gaggawa.
Kamar yadda rahoton Channels TV ya nuna, shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ne ya karanta wasikar Shugaba Tinubu a sauran majalisar.
Dalilin ƙara wa'adin kasafin kudin 2023
A nasa bangaren, jagoran majalisar, Opeyemi Bamidele ya nemi majalisar dattawan da ta dakatar da dukkanin wasu dokokinta domin tsawaita wa'adin kudurorin dokar kasafin.
Opeyemi Bamidele ya ce:
"Idan ba a manta ba, a ranar 20 ga watan Maris din 2024 aka sabunta wadannan kudurorin domin tabbatar da aiwatar da ayyukan da ke a kasafin kudin kasar na 2023.
"Tsawaita wa'adin amincewa da kudurorin zai taimaka wajen ganin an aiwatar da ayyukan da ba a karasa ba, kuma wa'adin zai kare ranar 30 ga watan Yunin 2024."
Bukatar Tinubu ta jawo hayaniya a majalisa
A wani labarin, mun ruwaito cewa bukatar da shugaban kasa Bola Tinubu ya gabatarwa majalisar dattawa na tsawaita wa'adin aiwatar da kasafin 2023 ya jawo cece-kuce a majalisar.
Shugaban marasa rinjaye na majalisar, Kingsley Chinda ya nuna cewa ba daidai ba ne a ce Najeriya tana tafiyar da kasafin kudi uku zuwa hudu a lokaci guda.
Asali: Legit.ng