Matasa Sun Shiga Babbar Matsala Sanadin Facebook, Ana Neman Su Biya N100m

Matasa Sun Shiga Babbar Matsala Sanadin Facebook, Ana Neman Su Biya N100m

  • Wasu matasa a jihar Abia na kokarin fadawa babbar matsala sakamakon amfani da kafar Facebook ta hanyar da ba ta dace ba
  • Matasan biyu sun yi rubutu kan cewa an kori wata ma'aikaciyar gwamnatin Abia kan wawushewa jihar Abia makudan kudi
  • Saboda haka ne ma'aikaciyar mai suna Lady Joy Maduka ta shigar da kara gaban kotu domin bata mata suna da matasan suka yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Abia - Wasu matasa na kokarin fadawa cikin matsala bayan sun zargi sakatariyar dindindin a ma'aikatar muhalli ta jihar Abia da rashawa.

Matasan su biyu sun yi rubutu a kafar Facebook da cewa an kori sakatariyar, Lady Joy Maduka daga aiki ne biyo bayan cin hanci da aka kamata ta yi.

Kara karanta wannan

Ruwa ya cinye wasu dalibai a hanyarsu ta dawo wa daga jarrabawa a Kaduna

Kotu Abia
Ana neman matasa su biya N100m saboda zargin bata suna. Hoto: Witthaya Prasongsin
Asali: Getty Images

Jaridar Tribune ta ruwaito cewa a sanadiyyar haka ne Lady Joy Maduka ta nemi kotu ta karbo mata hakkinta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Menene matasan suka rubuta a Facebook?

Biyo bayan sallamar Lady Joy Maduka daga aiki sai matasan suka rubuta cewa an kore ta ne saboda ta yi sata.

Matasan sun rubuta a Facebook cewa Lady Joy Maduka ta karkatar da kudi kimanin Naira miliyan 23 daga wajen aikinta.

Abin da Lady Joy ke buƙata daga matasan

Nan take Lady Joy Maduka ta shigar da kara babbar kotun jihar Abia kan cewa matasan sun ɓata mata suna, rahoton Vanguard.

Ta bukaci kotun ta tilastawa matasan biyanta kudi Naira miliyan 100 da kuma neman afuwarta a manyan jaridun Najeriya guda biyu.

An sallami Lady Joy daga aiki

A ranar 21 ga watan Yuni ne gwamnatin jihar Abia ta fitar da takardar sallamar Lady Joy Maduka daga aiki.

Kara karanta wannan

Kungiyar kwadago ta dauki mataki bayan Tinubu ya yi biris da maganar ƙarin albashi

Sai dai a cikin takardar gwamnatin ba ta bayyana dalilin da yasa aka sallami Lady Joy Maduka daga aiki ba.

An kama dilolin kwaya a Katsina

A wani rahoton, kun ji cewa hukuma mai yaki da safarar miyagun kwayoyi ta kasa ta bayyana nasarorin da ta samu cikin shekara daya a Katsina.

Rahotanni sun yi nuni da cewa NDLEA ta yi nasarar cafke dilolin kwaya da masu safarar ta zuwa kasashen ketare da dama cikin wannar shekarar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Online view pixel