Kano: Adadin Mutanen da Suka Mutu Sakamakon Harin da Aka Kai Masallaci Ya Ƙaru
- Adadin Musulman da suka rasu sakamakon harin masallacin da wani mutumi ya kai a jihar Kano ya ƙaru zuwa 23
- Bincike ya nuna cewa mutum 22 daga cikin 24 da aka kwantar a asibitin Murtala Muhammad sun rasu, wani mutum ɗaya ya rasu asibitin Aminu Kano
- Shafiu Abubakar, ɗan shekara 38 ne ya bankawa masallacin wuta a lokacin da Musulmai ke tsaka da Sallar asuba a Larabar Abasawa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kano - An samu ƙarin mutanen da suka rasu sakamakon harin da wani matashi ya kai Masallaci a Larabar Abasawa, karamar hukumar Gezawa a Kano.
Shafi’u Abubakar, ɗan kimanin shekaru 38 ne ya bankawa Masallacin wuta yayin da mutane ke tsaka da Sallar Asubah a watan Mayun da ya gabata.
A wani bincike, jaridar Daily Trust ta gano cewa adadin waɗanda suka rasu sakamakon ibtila'in sun ƙaru zuwa 23.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mutum 23 sun rasu a harin masallacin Kano
Binciken da aka yi a asibitin Murtala Muhammad, inda aka kwantar da waɗanda suka jikkata, ya nuna cewa 22 daga cikin mutum 24 sun mutu.
Mutum daya da aka kai Asibitin Koyarwa na Aminu Kano shi ma ya mutu sakamakon raunuka da ya ji, hakan ya sa adadin wadanda suka mutu ya zama 23.
Akwai wanda ya kwance a AKTH Kano
An tattaro cewa har yanzun akwai ragowar mutum ɗaya da ke kwance a asibiti yana jinya, an sallami ɗaya ya koma gida, sai kuma mutum biyu da suka tsira daga harin.
Ana zargin Shafiu Abubakar ya yi amfani da fetur, ya wanke masallacin tare da kulle ƙofofi, sannan ya cinnawa masallata akalla 30 wuta suna cikin Sallar asuba.
Bayan aikata wannan ɗanyen aiki, wanda ake zargin ya shaidawa ƴan sanda cewa ya yi haka ne domin hukunta waɗanda yake zargin sun zalunce shi a rabon gadon gidansu.
Kano: An gurfanar da Shafi'u gaban kotu
Tuni dai aka gurfanar da wanda ake zargin a gaban wata kotun shari’ar Musulunci karkashin jagorancin Mai Shari'a Halhalatu Zakariyya.
Bayan haka ne kotun ta bayar da umarnin a tsare shi a gidan gyaran hali kafin zama na gaba.
Ƴan bindiga sun sace shanun Liman
A wani rahoton kuma Ƴan bindiga sun kai hari kauyen Gidan-Makera a ƙaramar hukumar Kagarko da ke jihar Kaduna, sun tafi da shanun babban limamin garin.
Mazauna yankin sun bayyana cewa wasu ƴan banga sun yi nasarar kwato shanun bayan sun bi bayansu ranar Talata.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng