Duk da Gargadin Abba, An Kafa Tuta a Fadar Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero

Duk da Gargadin Abba, An Kafa Tuta a Fadar Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero

  • Rikicin sarautar Kano na kara kamari yayin da aka hango tutar sarauta a fadar sarki da ke Nassarawa a safiyar Alhamis a wani sabon salo
  • Tutoci biyu aka nada a fadar, da su ka hada da na sarauta da kuma na Najeriya, wanda hakan ke nuna iko da izzar sarki a duk inda ya ke
  • Duk da har yanzu gwamnatin Kano ba ta ce komai a hukumance kan al'amarin ba, darakta janar na gwamnan ya magantu kan batun a shafin facebook

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano- Rikicin masarautar Kano na kara kamari yayin da aka hango fadar Nassarawa ta kafa tutar sarauta.

Kara karanta wannan

Aure mai dadi: Mawaki Davido gwangwaje amaryarsa da kyautar motar alfarma

Da sanyin safiyar yau Alhamis aka hango tutocin sarauta da na Najeriya na lulawa daga fadar Sarkin Kano na 15 da ke Nassarawa.

Aminu Ado Bayero
Fadar Sarki na 15 ta dora tutar mulki Hoto: Aminu Ado Bayero
Asali: Facebook

Daily Trust ta wallafa cewa tutar na nuna iko da mulki na sarki a duk inda aka ga an saka shi, kuma sai sarki ya na nan ake dorawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Aikin sa tutoci a fadar Aminu Ado Bayero

Rahotanni sun bayyana cewa tun a yammacin Laraba aka fara aikin sanya tutar, inda aka fara da saka falwaya.

Da misalin 6.00am na safiyar Alhamis ne kuma aka dora tutar a wani yunkuri na nuna izza, kuma ana daga tutuocin safiya, a sauke su da yamma.

Gwamnatin Kano ta tanka Aminu Ado Bayero?

Duk da gwamnatin jihar Kano ba ta ce komai kan lamarin ba a hukumance, amma darakta janar na gwamna kan yada labarai, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya tofa albarkacin bakinsa.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta ware N1bn domin muhimman ayyuka a bangaren lafiya

A wani dan rubutun hoto da ya wallafa a shafinsa na facebook, ya na ganin daga tutar da sanya ta makabarta bai dace ba.

A baya gwamnatin Kano ta bukaci Aminu Ado Bayero ya fice daga gidan Nasarawa.

An tura jami'an tsaro fadar sarakuna

A wani labarin kun ji cewa an kara tura jami'an tsaro fadar sarakunan Kano domin kara karfafa tsaro yayin da ake rikici kan waye sarki.

Kwamishinan 'yan sandan Kano, Muhammad Usaini Gumel ya ce an tura karin jami'an ne domin tabbatar da kare lafiyar dukkan sarakunan.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Online view pixel