Gwamnoni 36 Sun Yi Taron Gaggawa a Abuja, an Bayyana Abubuwan da Aka Tattauna

Gwamnoni 36 Sun Yi Taron Gaggawa a Abuja, an Bayyana Abubuwan da Aka Tattauna

  • A jiya Laraba ne dukkan gwamnonin Najeriya su 36 suka yi taro a birnin tarayya Abuja domin tattauna matsalolin da kasar ke fuskanta
  • Gwamnonin sun tattauna kan abubuwa da dama sai dai an gano cewa sun mayar da hankali kan maganar ƙarin albashi da yancin kananan hukumomi
  • Wasu daga cikin gwamnonin sun bayyana dalilan kin amincewa da karin albashi da gwamnatin tarayya da yi ga kungiyar kwadago

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Gwamnonin Najeriya sun yi taro a Abuja domin tattaunawa kan matsalolin da kasar ke fama dasu.

Rahotanni sun nuna cewa taron ya mayar da hankali ne kan karin albashi da maganar yancin kananan hukumomi.

Kara karanta wannan

Gwamnoni 36 sun gana a Abuja, sun cimma matsaya kan sabon mafi ƙarancin albashi

Gwamnonin Najeriya
Gwamnoni sun yi bayani kan karin albashi. Hoto: Abdul No Shaking
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa wasu daga cikin gwamnonin sun yi turjiya kan yarda da mafi ƙarancin albashin da gwamnatin tarayya ta ayyana.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tattaunawar gwamnoni kan karin albashi

Har yanzu wasu daga cikin gwamnoni sun ki amincewa da N62,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashi kamar yadda gwamnatin tarayya ta mika tayi ga 'yan kwadago.

Sun bayyana matsin tattalin arziki da ake ciki da kuma cewa wasu jihohin sai sun ci bashi kafin su iya biyan albashi a matsayin dalilin kin amincewa.

Sai dai jaridar Punch ta ruwaito cewa rahoton karshen taron ya nuna kungiyar gwamnonin ta ce za ta fitar da matsaya kan karin albashi da za ta faranta ran ma'aikata.

Yancin ƙananan hukumomin jihohin Najeriya

Har ila yau taron gwamnonin ya mayar da hankali kan yadda za a samu mafita wajen dambarwar da ake a kan yancin kananan hukumomi.

Kara karanta wannan

Gwamna ya yi magana kan yunƙurin tashin bam, ya fallasa masu ɗaukar nauyi

A yanzu haka dai maganar yancin ƙananan hukumomi tana gaban kotu kamar yadda gwamnatin tarayya ta shigar da gwamnonin kara.

Wasu gwamnoni sun tura wakilai

Gwamnonin jihohi da dama sun halarci taron da kansu domin tattaunawa a kan yadda za a samar da mafita a Najeriya.

Sai dai kuma an ruwaito cewa gwamnonin jihohin Borno da Akwa Ibom sun tura mataimakansu ne yayin taron.

Kotu ta yi matsaya kan kananan hukumomi

A wani rahoton, kun ji cewa kotu ta dauki mataki game da shari'ar da ake yi tsakanin Gwamnatin tarayya da kuma gwamnonin jihohi 36 a Najeriya.

Rahotanni sun yi nuni da cewa kotun koli ta tanadi hukunci kan shari'ar inda ta bukaci duka bangarorin su saurari ranar da za ta tuntube su.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Online view pixel