Gwamnoni 36 Sun Gana a Abuja, Sun Cimma Matsaya Kan Sabon Mafi Ƙarancin Albashi

Gwamnoni 36 Sun Gana a Abuja, Sun Cimma Matsaya Kan Sabon Mafi Ƙarancin Albashi

  • Gwamnoni 36 na Najeriya sun tabbatar da cewa ma'aikata za su samu ƙarin albashi mai tsoka a tattaunawar da ake yi
  • AbdulRahman AbdulRazaq na jihar Kwara ne ya bayyana haka bayan taron ƙungiyar gwamnoni wanda ya gudana ranar Laraba
  • A cewar gwamnonin, za su ci gaba da tuntuɓar masu ruwa da tsaki domin ganin an cimma matsayar da kowa zai yi farin ciki da ita

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Gwamnonin jihohi 36 sun kammala taron da suka kira kan sabon mafi ƙarancin albashin ma'aikata da wasu batutuwa da suka shafi ƙasa.

Gwamnonin karƙashin ƙungiyarsu NGF sun tabbatarwa ma'aikata cewa su sha kurimunsu, za su samu ƙarin albashi mai tsoka idan aka ƙarƙare tattaunawa.

Kara karanta wannan

Shettima ya sa labule da gwamnoni kan sabon mafi ƙarancin albashi da wasu batutuwa

Gwamnonin Najeriya.
Gwamnoni sun tabbatarwa ma'aikata za su samu mafi kyau albashi idan aka gama tattaunawa Hoto: @NGFSecretariat
Asali: Facebook

Wace matsaya gwamnoni suka amince da ita?

A taron a suka gudanar a Abuja ranar Laraba, gwamnonin sun amince za su ci gaba da tuntubar masu ruwa da tsaki domin cimma matsaya, Channels tv ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sun bayyana matsayar da suka cimma a zaman ne a wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun shugaban gwamnonin Najeriya kuma gwamnan Kwara AbdulRahman AbdulRasaq.

A rahoton Punch, sanarwan ta ce:

"Gwamnonin jihohi sun amince za su ci gaba da tuntuɓar manyan masu ruwa da tsaki domin cimma matsayar da ta dace.
"Muna sane da matakan da ake bi kuma muna goyon baya tare da tabbatar da cewa ma'aikata za su samu albashi mai tsoka daga tattaunawa da ake ci gaba da yi."

FEC fa jingine batun karin albashi

Wannan na zuwa ne sa'o'i 24 bayan majalisar zartaswa ta tarayya (FEC) ƙarƙashin Bola Tinubu ta ɗage tattaunawa kan batun sabon mafi ƙarancin albashi.

Kara karanta wannan

Gwamnoni 36 sun yi taron gaggawa a Abuja, an bayyana abubuwan da aka tattauna

Jim kaɗan bayan kammala taron FEC, ministan yaɗa labaru Mohammed Idris ya ce majalisar ta jingine rahoton ƙarin albashi domin bai wa Tinubu damar ci gaba da tuntuɓar waɗanda lamarin ya shafa.

A cewarsa, ba zai yiwu su ɗauki matsaya ba saboda batu ne da ya shafi ƙananan hukumomi, jihohi, ƴan kwadago da kamfanoni masu zaman kansu.

Bugu da ƙari, an ji gwamnonin sun tattauna kan wasu batutuwan da suka shafi kasar nan kamar tsare-tsaren kasafin kudi da kuma sake fasalin karɓar haraji.

Wani ma'aikacin gwamnati a jihar Katsina, Abdul Ahmad ya shaidawa Legit Hausa cewa sun gaji da jin gafara sa ba su ga ƙaho ba kan batun ƙarin albashi.

A cewarsa, gwamnoni da yawa sun yi alƙawarin ƙarin albashi na wata uku bayan cire tallafin mai amma sun gaza cikawa har kawo yanzu.

"Ba a nan gizo ke saƙa ba sai bayan an cimma matsaya za ka ji sun yi gum. Alal misali ba zan ambaci suna ba amma akwai gwamnan da ya yi alƙawarin ƙarin kuɗi bayna cire tallafi amma har yau shiru."

Kara karanta wannan

Bola Tinubu zai gana da gwamnoni, za su tattauna kan mafi ƙarancin albashi a Aso Villa

Gwamnatin tarayya ta gana da ASUU

A wani rahoton Gwamnatin Bola Tinubu ta fara zaman tattunawa da ASUU domin shawo kanta ta hakura da shiga yajin aiki a jami'o'in Najeriya.

Ministan ilimi na kasa, Farfesa Tahir Mamman, ya ce yana da yaƙinin za su warware buƙatun ƙungiyar ba tare da an kai ruwa rana ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262