ASUU Ta Tsorata Gwamnatin Bola Tinubu, An Fara Zaman Tattaunawa a Abuja

ASUU Ta Tsorata Gwamnatin Bola Tinubu, An Fara Zaman Tattaunawa a Abuja

  • Gwamnatin Bola Tinubu ta fara zaman tattunawa da ASUU domin shawo kanta ta hakura da shiga yajin aiki a jami'o'in Najeriya
  • Ministan ilimi, Farfesa Tahir Mamman, ya ce yana da yaƙinin za su warware buƙatun ƙungiyar cikin ruwan sanyi
  • Ƙungiyar ASUU dai ta yi barazanar tsunduma yajin aiki matuƙar gwamnati ba ta tashi tsaye, ta biya mata buƙatunta ba

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Gwamnatin tarayya ƙarƙashin shugabancin Bola Ahmed Tinubu ta fara tattaunawa da shugabannin kungiyar malaman jami’o’i ta ƙasa (ASUU).

Gwamnatin ta fara zaman tattaunawa da ASUU ne domin daƙile yunƙurinta na garƙame jami'o'in Najeriya da tsunduma yajin aikin sai baba-ta-gani.

Kara karanta wannan

Ana cikin matsalar rashin tsaro, Shettima ya fadi shirin Tinubu kan 'yan bindiga

Shugaban ASUU da Bola Ahmed Tinubu.
Gwamnatin tarayya ta fara zaman tattaunawa da ƙungiar ASUU Hoto: ASUU, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Yadda zaman ASUU da gwamnati ya kaya

Ministan ilimi, Farfesa Tahir Mamman ya bayyana cewa yana da ƙwarin guiwar za su cimma maslaha tsakaninsu da ASUU cikin ruwan sanyi, Channels tv ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Farfesa Tahir Mamman ya faɗi haka ne yayin zantawa da manema labarai jim kaɗan bayan fitowa daga ganawarsa da ASUU a ma'aikatar ilimi da ke Abuja ranar Laraba.

Kungiyar ASUU tayi maganar yajin-aiki

A nasa bangaren, shugaban ASUU na ƙasa, Farfesa Emmanuel Osodoke, ya ce gwamnati za ta iya hana malaman jami'o'i shiga yajin aiki idan ta yi abin da ya dace.

An san malaman jami'a da yawan zuwa yajin-aiki saboda zargin saba alkawari.

Wace barazana kungiyar ASUU ta yi?

A makon jiya ASUU ta reshen jami'ar tarayya da ke Gashua a Yobe ta roki gwamnatin tarayya ta hanzarta warware matsalolin ƙungiyar idan ba ta son ilimi ya tsaya cak a jami'o'i.

Kara karanta wannan

Emefiele: Bayan ƙwace kadarorin N12bn, tsohon gwamnan CBN ya nemi alfarma a kotu

Shugaban ƙungiyar reshen na Gashuwa, Melemi Abatcha, ne ya faɗi haka a wata hira da ƴan jarida ranar Alhamis da ta shige a Damaturu.

A cewarsa, kudin farfaɗo da jami'o'in gwamnati da kuma sake zama kan yarjejeniyar 2009 sune manyan batutuwan da ke kawo cikas a harkar ilimi.

Wani muhimmin batu da ASUU ta jima tana buƙatar gwamnatin tarayya ta aiwatar shi ne bai wa jami'o'i damar cin gashin kansu, cewar rahoton Vanguard.

Fadar shugaban kasa ta sayo tayoyi

Kun da labarin cewa duk da matsin rayuwar da ake ciki a Najeriya, fadar shugaban kasa ta kashe miliyoyin Naira wajen sayen tayar motoci.

Wani bincike ya gano cewa an sayi tayoyin mota masu sulke da wadansu tayoyin da ba a san adadinsu ba kan makudan kudi N244,654,350.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel