Ruwa ya Cinye Wasu Dalibai a Hanyarsu ta Dawo wa Daga Jarrabawa a Kaduna

Ruwa ya Cinye Wasu Dalibai a Hanyarsu ta Dawo wa Daga Jarrabawa a Kaduna

  • Mazauna kauyen Ribang sun shiga bakin ciki bayan rasuwar yaransu guda shida a hanyarsu ta dawo wa daga makaranta a yammacin Talata
  • Jami'in yada labaran kungiyar ci gaban yankin Ribang na kasa, Fasto Simon Ishaku ya ce dama kogin Mbang ya dade ya na masu barna
  • Faston ya roki gwamnan jihar Kaduna da wakilinsu a majalisar dokoki su taimaka wajen gina gada da hanya mai kyau ga mutanen yankin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Kaduna- An shiga alhini bayan wasu dalibai sun rasa rayukansu a jihar Kaduna yayin da su ke komawa gida bayan kammala jarrabawar WAEC.

Daliban 'yan aji uku na karamar sakandare sun rasu ne a kogin Mbang da ke Ribang a karamar hukumar Kauru a jihar Kaduna.

Kara karanta wannan

An shiga rudani, 'yan ta'adda sun lafta harajin wata wata a kan mazauna Binuwai

Uba Sani
Ruwa ya cinye dalibai a Kaduna Hoto; Senator Uba Sani
Asali: Facebook

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa daliban na hanyar komawa ga iyayensu cike da murna bayan kammala jarrabawar da misalin karfe 5.30pm a lokacin da iftila'in ya fada masu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana kokawa da kogin Mbang a Kaduna

Ruwan kogin Mbang ya cinye dalibai guda shida a hanyarsu ta koma wa gida; daliban sun hada da Manasseh Monday, Musa John, Pius David, Monday Ayuba, David Danlami da Yahuza Audu.

Mazauna yankin sun bayyana cewa kogin ya dade ya na cinye jama'ar garin, lamarin da ke ci masu tuwo a kwarya, kamar yadda jaridar Punch a wallafa.

Jami'in yada labaran kungiyar ci gaban yankin Ribang na kasa, Fasto Simon Ishaku dole sai mazauna garin sun yi tafiya mai nisa kafin su je makaranta ko asibiti.

Ya roki gwamnan jihar, Uba Sani da dan majalisar da ke wakiltarsu, Sunday Katung su taimaka masu da gina asibiti, makaranta, gada da hanya mai kyau a yankin.

Kara karanta wannan

Aure mai dadi: Mawaki Davido gwangwaje amaryarsa da kyautar motar alfarma

El Rufa'i ya maka majalisar Kaduna kotu

A wani labarin kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El Rufa'i ya maka majalisar dokokin jihar gaban kotu kan zargin badakala a gwamnatinsa.

Tsohon gwamnan ya na neman kotu ta rushe rahoton da majalisar ta fitar na cewa gwamnatinsa ta yi almundahanar Naira Biliyan 432 domin ba a ba shi damar kare kansa ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Online view pixel