Bidiyo: Wata Mata Ta Nemi Taimakon Ƴan Arewa, Ta Faɗi Yadda Wani Mutumi Ya Cuce Ta

Bidiyo: Wata Mata Ta Nemi Taimakon Ƴan Arewa, Ta Faɗi Yadda Wani Mutumi Ya Cuce Ta

  • Wata mai dafa abinci a jihar Bauchi ta shiga matsala yayin da wani ya ba ta kwnagilar dafa abincin sadaka kuma ya gudu
  • A faifan bidiyo, Hajiya Aisha ta bayyana cewa ta girka abincin karin kumallo, na rana da tuwon dare na mutum 9,800 kuma yanzu ta rasa yadda za ta yi da shi
  • Ta yi kira ga manyan Arewa su taimaka su sayi abincin domin ta samu ta biya basukan mutane da ta karɓo

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Bauchi - Wata mai gidan abinci a jihar Bauchi, Hajiya Aisha, ta yi kira ga manyan Arewa su kawo mata agaji kan wata kwangilar abinci da aka barta da shi.

Kara karanta wannan

Yobe: Wata matar aure ta soka wa mijinta wuƙa har lahira, ta yi bayanin abin da ya faru

Matar ta bayyana cewa wani mutumi ne ya kira ta, ya buƙaci ta girka abincin mutane sama da 9,000 da za a raba kyauta ga mabuƙata a kananan hukumomi uku.

Hajiya Aisha Mai Abinci.
Yadda wani mutumi ya cuci mai abinci a jihar Bauchi Hoto: Barde Kerarren Ajiya
Asali: Facebook

Shafin Barde Kerarren Ajiya ne ya wallafa bidiyon matar a Facebook ranar Talata da daddare.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda mutumin ya cuci Hajiya Aisha

A faifan bidiyon, an ji Hajiya Aisha na bayanin yadda mutumin ya tuntuɓe ta kan girka abincin mutum 9,800, amma daga ƙarshe ya daina ɗaukar kiranta.

A cewarta, ta yi ƙoƙarin ganin mutumin ya ba ta takardar yarjejeniyar kwangilar dafa abincin amma ya roƙi ta ci gaba da aikin kafin ya gama shirya komai.

"Na gamu da darasin rayuwa, jiya wani ya kirani na dafa abincin mutum 9,800 da za a raba a kananan hukumomi uku, na yi na yi ya bani yarjejeniya amma ya ce mu ci gaba da aiki.

Kara karanta wannan

"Ban san Aminu Ado ba": Kwamishinan 'yan sanda ya fadi matsayarsa kan rigimar Kano

"Tun karfe 9:00 na safe na gama nake ta kiransa amma bai ɗaga ba, na je ofis na same shi, ya faɗa mun na ƙara haƙuri yana jiran umarni ne daga sama. Bayan na dawo na kara kiranshi amma ba ya ɗagawa.
"A karshe na faɗawa mijina muka je ofishinsu amma muka taras ba ya nan, idan an kira wayarsa ba ya ɗagawa, ga shi an barni da abinci mai yawa har dare ya yi, Dan Allah a taimaka mun."

- Hajiya Aisha.

Matar ta bayyana cewa bashi ta runtumo ta yi aikin saboda ko kwandala ba a ba ta na kafin alƙalami ba.

Sakamakon haka ta yi kira ga manyan Arewa su agaza mata su sayi abincin ko dan ta samu kuɗin da za ta biya bashin da ta runtumo.

Mutane sun mayar da martani

Jamilan Baba Buhari ta ce:

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un wannan wane irin zalinci ne wannan baiwar Allah ina za ta sa kanta. Allah ya kawo miki dauki."

Kara karanta wannan

Kwantai: Wani bawan Allah ya ceto Aisha mai abinci daga tafka asara a Bauchi

Hon Sale Nabayi ya ce:

"Hasbunallahu wa ni'imal wakeel, wannan wane irin abu ne. Shawari na ki yi maza ki raba abincin ga bayin Allah in sha Allah, Allah zai baki mafita cikin karamin lokaci domin zai lalace Hajiya."

Zayyad JD Hassan ya ce:

"Ya kamata ku faɗi abincin na nawa ne domin kila wani zai iya saya."

An raba matar da abinci

Daga baya labari ya zo cewa wani Bawan Allah ya taimakawa wannan mata, ya saye gaba daya abincin da aka nemi a bar ta da shi.

Kwamred Ameen Sulaiman ya wallafa bidiyon rabon abincin a shafin Facebook inda aka gane cewa an raba ta da yin kwantan shi.

Mata sun yi zanga-zanga a Rivers

Kuna da labarin wasu fusatattun mata sun shiga zanga-zanga domin nunawa mahukunta bacin ransu na rashin wuta da su ke fama da shi a yankunansu a jihar Ribas.

Matan da su ka fito daga yankin Ipo sun bayyana cewa wannan ba shi ne karon farko da su ka fito domin neman a agaza masu kan batun karancin wuta.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262