An Shiga Rudani, 'Yan Ta'adda Sun Lafta Harajin Wata Wata a Kan Mazauna Binuwai

An Shiga Rudani, 'Yan Ta'adda Sun Lafta Harajin Wata Wata a Kan Mazauna Binuwai

  • An shiga halin dar-dar bayan yan ta'adda sun fara tilastawa mazauna Binuwai bayar da harajin wata-wata domin tsira da rayukansu
  • Wasu mazauna jihar da su ka zanta da manema labarai sun bayyana cewa 'yan ta'addar na neman tara N20m daga gidajen da ke yankin Ukum
  • Shugaban riko na karamar hukumar Ukum, Victor Lorzaa ya tabbatar da mummunan al'amarin, inda ya ce tuni ya shaidawa jami'an tsaro

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Benue- Al'umar karamar hukumar Ukum a jihar Binuwai sun bayyana cewa su na cikin kangin rayuwa bayan 'yan bindiga sun tilasta masu bayar da harajin wata-wata.

Wasu da su ka shaidawa manema labarai halin da su ke ciki sun ce yanzu haka 'yan ta'adda sun fara karbar haraji daga hannun mazauna kauyen Torough da sauran kauyuka.

Kara karanta wannan

Yan ta'adda sun mamaye fitaccen gari a Zamfara, dan majalisa ya nemi dauki

Benue
Yan bindiga sun fara karbar haraji a Binuwai Hoto; Legit.ng
Asali: Original

'Yan bindiga sun addabi Binuwai

Vanguard News ta wallafa cewa 'yan bindigar su na tilasta wa kowane gida biyan harajin N20m, kuma babu wanda ya isa ya tanka masu, dole a bayar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wuraren da ayyukan yan ta'addan ya yi kamari na karbar haraji sun hada da Sankera, Logo, Ukum da Katsina Ala.

"Mun san masu karbar harajin," Victor Lorzaa

Shugaban riko na karamar hukumar Ukum a jihar Binuwai, Victor Lorzaa ya tabbatar da cewa 'yan bindiga sun fara tilastawa jama'arsa bayar da haraji.

Mista Lorzaa ya ce ya na tabbacin labarin miyagun sun fara karbar kudin fansa, yayin da su ka nemi a biya su N20m, kamar yadda Daily Post ta wallafa.

Shugaban rikon ya sanar da cewa yanzu haka ya sanar da jami'an tsaro halin da ake ciki, inda ya ce wani kasungurmin dan ta'addan kungiyar 'Full Fire' ne ke karbar kudin.

Kara karanta wannan

IPMAN: Farashin litar man fetur ya kai N2,000 a jihar Arewa, an gano dalilin tashin

Rahotanni sun nuna cewa yan bindigar na karbar N50,000 da N1m daga hannun wasu daga cikinsu, yayin da su ke neman N20m.

Mahara sun farmaki mazauna Binuwai

A wani labarin kun ji cewa wasu mahara a kan babura sun kai hari kauyen Gugur a karamar hukumar Katsina Ala da ke jihar Binuwai inda su ka kashe mutane da dama.

Dan majalisar jiha da ke wakiltar yankin, Jonathan Agbidye ya tabbatar da harin da ya ce na ramuwar gayya ne, kuma mutane shida ake fargabar sun mutu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.