Zargin Tsige Sarkin Musulmi: Majalisa Ta Gabatar da Kudirin Sabunta Dokar Masarautar Sokoto

Zargin Tsige Sarkin Musulmi: Majalisa Ta Gabatar da Kudirin Sabunta Dokar Masarautar Sokoto

  • Kudurin yin garambawul ga dokar Masarautar Sokoto ya tsallake karatu na daya da na biyu a zauren majalisar dokokin jihar Sokoto
  • Idan har aka tabbatar da wannan sabuwar dokar, ana fargabar hakan zai rage karfin ikon Mai Alfarma Alhaji Sa'ad Abubakar III
  • Wannan na zuwa ne kwanaki kadan bayan da kungiyar MURIC ta zargi gwamnatin Sokoto da yunkurin tube rawanin Sarkin Musulmi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Sokoto - A zaman majalisar jihar Sokoto na ranar Talata, an ruwaito cewa kudurin da zai yi gyara ga dokar masarautarya tsallake karatu na farko da na biyu.

An ce sabuwar dokar za ta rage karfin ikon Mai alfarma Alhaji Sa'ad Abubakar III, wanda ya haɗa da cire ikon naɗa hakimai ko masu naɗin sarki ba tare da izinin gwamnatin jihar ba.

Kara karanta wannan

Gwamma ya faɗi gaskiya kan shirin tsige Mai aAfarma Sarkin Musulmi a Najeriya

Majalisar zartarwa ta gabatar da kudirin sabunta dokar masarautar Sokoto
Kudirin sabunta dokar masarautar Sokoto ya tsallake karatu na biyu. Hoto: @Ahmedaliyuskt
Asali: Twitter

MURIC na zargin tsige sarkin Musulmi

A cewar jaridar The Punch, ƙudurin dokar ya tsallake karatu na biyu ne kwanaki kadan bayan kungiyar MURIC ta zargi gwamnatin Sokoto da yunkurin tsige sarkin Musulmi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban ƙungiyar MURIC, Farfesa Isiaq Akintola ya bayyana damuwarsa kan wani yunkuri na Gwamna Ahmed Aliyu na tube rawanin Mai alfarma, Abubakar Sa'ad III.

Kungiyar musuluncin ta ce matsayin Sarkin Musulmi ya zarce al'ada kawai domin al'ummar Musulmi a ƙasar na kallonsa matsayin jagoransu gaba daya, in ji rahoton Parallelfacts.

Kudurin sabunta dokar masarautar Sokoto

Kamar yadda wani rahoton BBC Hausa ya nuna, kudurin dokar da majalisar zartarwar jihar ya gabatar wa majalisa ya jawo cece-kuce, yayin da ake muhawara a kai.

A taron majalisar zartarwar Sokoto na biyar a 2024, an amince da yin gyara ga dokar kananan hukumomin jihar ta shekarar 2008.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Muhammadu Sanusi II ya gana da fitaccen malamin Musulunci a fadar Sarkin Kano

Za a yi gyara musamman ga kashi na biyu na sashe na 76 na dokar masarauta, wanda ya ba Sarkin Musulmi ikon naɗa hakimai da masu nadin sarki.

Sabunta dokar za ta sa majalisar sarkin Musulmi ta rika gabatar da bukatar nada wadanda ake so a matsayin uwayen kasa ga gwamna domin neman amincewa.

Atiku ya tsawatarwa gwamnoni kan masarautu

A wani labarin, mun ruwaito cewa Atiku Abubakar ya nemi gwamnonin Najeriya da su kare martabar masarautu ba wai su yi kokarin ruguza su ba.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya yi kira da a yi gyara ga kundin tsarin mulkin Najeriya domin ba da damar sanya masarautu a cikin dokar ƙasar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel