Gwamnatin Abba Gida Gida ta Sake Ware N600m Domin Ayyukan Cigaban Kano
- Gwamnatin Abba Gida-gida a Kano ta sake ware wasu makudan kudi jim kadan bayan fitar da Naira Biliyan 1 domin gudanar da ayyukan ci gaba a fadin jihar
- An fitar da N600m wanda ke a matsayin kasonta na gudanar da ayyukan ci gaba da kungiyoyi masu zaman kansu a jihar, inda ya nemi hadin kansu wajen ayyukan
- Gwamnan wanda ya samu wakilcin shugaban ma'aikatan fadar gwamnati, Shehu Wada Sagagi ya ce matukar kungiyoyin su ka lura za a yi ba daidai ba, su sanar da su
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano- Gwamnatin Kano ta bayyana fitar da N600m a matsayin kasonka na kudin gabatar da ayyukan ci gaba a jihar da hadin gwiwar kungiyoyi masu zaman kansu.
Haka kuma gwamnatin ta yi alkawarin bibiyar dukkanin ayyukan da ake gudanarwa a jihar wanda kungiyoyin ke yi domin tabbatar da gaskiya.
Punch News ta wallafa cewa darakta janar din gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya tabbatar mata da fitar da makudan kudin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnatin Kano ta nemi hadin kan kungiyoyi
Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya nemi hadin kan kungiyoyi masu zaman kansu domin tabbatar da an gudanar da ayyukan ci gaba yadda ya dace, kamar yadda Voice of Nigeria ta wallafa.
Gwamnan ya bayyana haka ne a taron tattaunawa da masu ruwa da tsaki kan ayyukan ci gaba a jihar, tare da tabbatar da gaskiya wurin gudanar da aikin yadda ya dace.
Gwamna Abba wanda ya samu wakilcin Shehu Wada Sagagi ya nemi kungiyoyin su sanar da ita duk wani rashin gaskiya wajen gudanar da ayyuka.
Abba ya kara da cewa sai sun sanar da shi ne za a samu damar daukar matakin da ya dace na hukunci domin hana afkuwar hakan a gaba.
Lafiya: Gwamnatin Kano ta ware N1bn
A baya mun ruwaito cewa gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta ware makudan kudi domin gudanar da ayyuka domin inganta bangaren lafiya.
Majalisar zartarwar jihar ce ta amince wa gwamnatin ta kashe N1bn wajen sayo magunguna da za a raba kyauta da ma gyara makarantu kan kiwon lafiya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng