NLC: Ƴan Kwadago Sun Roki Tinubu, Sun Faɗi Mafi Ƙarancin Albashin da Suke Buƙata

NLC: Ƴan Kwadago Sun Roki Tinubu, Sun Faɗi Mafi Ƙarancin Albashin da Suke Buƙata

  • Ƴan kwadago sun roki Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar da soyayyar da yake masu yayin yanke sabon mafi ƙarancin albashin ma'aikata
  • Mamban kwamitin mafi karancin albashi kuma wakilin NLC ya buƙaci shugaban ƙasa ya amince da buƙatar ƴan kwadago ta N250,000
  • A cewarsa, ma'aikata na shan wahala saboda tsadar rayuwar da aka shiga a ƙasar nan sakamakon tsare-tsaren gwamnatin tarayya

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Ƙungiyar kwadago ta yi kira ga Bola Ahmed Tinubu ya nuna ƙaunar da yake yiwa ma'aikata ta hanyar amincewa da N250,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashi.

NLC ta bayyana cewa hakan ne kaɗai zai sa ma'aikata su samu sauƙi duba da kunci da wahalhalun rayuwar da aka shiga a ƙasar nan.

Kara karanta wannan

Tinubu ya sake ɗauko tsohon kwamishinansa, ya naɗa shi a shirgegen muƙami

Shugabannin NLC da TUC.
NLC ta roki Bola Tinubu ya amince da N250,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashi Hoto: Nigera Labour Congress HQ
Asali: Twitter

Ɗaya daga cikin wakilan NLC a kwamitin mafi ƙarancin albashi kuma shugaban ƙungiyar ma'aikatan sufurin ruwa (MWUN), Prince Adewale Adeyanju ne ya faɗi haƙa yayin hira da Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kuma zargi gwamnonin jihohi da yunƙurin dakile kokarin da ake yi na samar da albashin da ya dace da rayuwar yanzu ga ma'aikatan gwamnati.

NLC ta roƙi Tinubu ya ɗauki N250,000

Adeyanju ya ƙara da cewa a halin yanzun wuƙa da nama na hannun mai girma shugaban ƙasa bayan kammala zaman kwamitin mafi karancin albashi, The Nation ta tattaro.

"Kowa ya san halin da ake ciki kuma ma'aikata na cikin ƙaƙanikayi. A ƙarshen tattaunawarmu mun cimma matsaya biyu, N62,000 daga ɓangaren gwamnati da kamfanoni da N250,000 daga ƴan kwadago."
"Wuƙa da nama na kan teburin shugaban kasa kuma wannan wata dama ce da zai nuna tausayawa ga ma'aikata. Sai bayan shekara biyar ake yin sabon albashi.

Kara karanta wannan

Sarkin Musulmi ya fadi lokacin da za a kawo karshen matsalar rashin tsaro a Arewa

"Shiyasa muke kira gare shi a matsayinsa na abokin ma'aikata wanda ya yi alƙawarin share masu hawaye, ya amince da N250,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashi."

- Adewale Adeyanju.

Tinubu ya nada shugaban FCCPC

A wani rahoton kuma Bola Ahmed Tinubu ya amince da naɗin Mr. Olatunji Bello a matsayin babban jami'im hukumar kula da abokan ciniki ta ƙasa (FCCPC).

Mai magana da yawun shugaban kasa, Ajuri Ngelale ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin, 24 ga watan Yuni, 2024.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262