Nakiya ta Tarwatsa mai Zanga Zanga Yayin da Rikicin Ribas ya Sauya Salo

Nakiya ta Tarwatsa mai Zanga Zanga Yayin da Rikicin Ribas ya Sauya Salo

  • Wani mai matsakaicin shekaru ya yi sanadiyyar kashe kansa a lokacin da ya ke kokarin tarwatsa nakiyar da ya ke dauke da ita lokacin zanga zanga a Ribas
  • Lamarin ya afku da safiyar Talata, inda magoya bayan Nyesom Wike ke zanga-zangar nuna rashin jin dadin yadda gwamna mai ci ya sutale wasu daga cikin masu mukamai
  • Gwamnan jihar, Siminalayi Fubara ya sauke shugabannin kananan hukumomi magoya bayan Wike da wa'adinsu ya cika, sannan ya tsige shugaban majalisar sarakuna

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Rivers- An wayi ranar Talata da fargaba a jihar Ribas bayan wani mai zanga-zanga ya tarwatsa kansa da nakiyar da ya ke dauke da ita.

Kara karanta wannan

Ruwa ya cinye wasu dalibai a hanyarsu ta dawo wa daga jarrabawa a Kaduna

Rahotanni sun bayyana cewa wani mutumi mai matsakaicin shekaru ne ya tarwatsa kansa a bakin otal din Hotel Presidential da misalin 9.45am.

Rivers
Nakiya ta hallaka mai dauke da ita yayin zanga-zanga a Ribas Hoto: Siminalayi Fubara, Nyesom Wike
Asali: Facebook

Nigerian Tribune ta wallafa cewa jami'an tsaro sun gaggauta zuwa wurin da iftila'in ya faru, kuma sun tafi da gawar mutumin yayin da jama'a ke cikin razani.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ribas: Masu zanga-zanga sun rufe hanya

'Yan zanga-zanga masu goyon bayan tsohon gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, kuma Ministan Abuja sun rufe hanyar zuwa Hotel Presidential a yau Talata.

Politics Nigeria ta wallafa cewa daga cikin masu zanga-zangar akwai shugabannin siyasa a mazabun Obio/Akpor inda su ka taru a cibiyar Rumueme Civic Centre.

Ana gudanar da zanga-zangar ne domin nuna rashin jin dadin yadda gwamnan jihar, Siminalayi Fubara ya tsige wasu magoya bayan Nyesom Wike daga muhimman mukamai.

Idan za a tuna Fubara ya fatattaki shugabannin kananan hukumomin jihar Ribas.

Kara karanta wannan

An shiga rudani, 'yan ta'adda sun lafta harajin wata wata a kan mazauna Binuwai

Fubara ya kori shugaban majalisar sarakuna

A baya mun kawo labarin cewa gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara ya kori shugaban majalisar sarakunan jihar Chidi Awuse tare da maye gurbinsa.

An maye gurbin Awuse wanda ke goyon bayan Nyesom Wike da Eze Chike Worlu Wodo bayan zarginsa da aka yi rashin iya shugabanci da tafiyar da lamurran sarauta.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.