Bidiyo: Muhammadu Sanusi II Ya Gana da Fitaccen Malamin Musulunci a Fadar Sarkin Kano
- Muhammadu Sanusi II ya ƙarbi bakuncin babban malamin addinin musulunci daga Maiduguri, jihar Borno, Sheikh Ali Abulfatahi
- Sheikh Abdulfatahi tare da tawagarsa sun kai wa Sanusi ziyara fadar Sarkin Kano ranar Litinin, 24 ga watan Yuni, 2024
- Wannan na zuwa ne a lokacin da ake ci gaba da taƙaddama kan sarautar Kano tun bayan rusa masarautu biyar da Abdullahi Ganduje ya kirƙiro
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano - Babban malamin addinin Musulunci a Maiduguri, jihar Borno, Khalifa Sheikh Ali Abulfatahi ya ziyarci mai martaba Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II.
Sarkin ya karɓi bakuncin fitaccen malamin da ƴan tawagarsa a fadarsa da ke Ƙofar Kudu a cikin kwaryar birnin Kano.
Hakan na ƙunshe ne a wani saƙo da masarautar Kano ta wallafa a shafinta na manhajar X wanda aka fi sani da Twitter ranar Litinin, 24 ga watan Yuni, 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Mai Martaba Sarkin Kano, Khalifa Muhammad Sanusi ll CON, ya karbi bakuncin Khalifa Sheikh Ali Abulfatahi daga Maiduguri."
Yadda aka fara rigimar sarautar Kano
Wannan ziyara na zuwa ne a daidai loƙacin da rigimar sarautar Kano ke ƙara ƙamari tsakanin Sanusi II da sarki na 15, Aminu Ado Bayero.
Idan ba ku manta ba Gwamna Abba Kabir Yusuf ya dawo da Sanusi II kan kujerar Sarkin Kano a watan Mayun 2024.
Sai dai wannan mataki bai yiwa Aminu Ado daɗi ba, wanda har yanzu yake zaune a ƙaramar fadar Nassarawa da ke cikin birnin Kano.
A makon jiya, babbar kotun tarayya mai zama a Kano rusa matakin dawo da Muhammadu Sanusi saboda Gwamna Abba ya take umarnin alƙali.
Hukuncin kotun ya bar baya da ƙura yayin da Gwamnatin Kano ta fito ta jaddada cewa Muhammadu Sanusi II na nan daram, ba wanda ya tsige shi.
Yan sanda sun girke jami'an tsaro
A wani rahoton kuma rundunar ƴan sanda ta bayyana dalilin da ya sa ta turan ƙarin jami’anta zuwa fadar da Muhammmadu Sanusi II da Aminu Ado Bayero.
Kwamishinan ƴan sandan jihar mai barin gado, AIG Usaini Gumel, ya bayyana cewa an tura ƙarin jami'an tsaron ne domin samar da tsaro a wuraren guda biyu.
Asali: Legit.ng