Tinubu Ya Sake Ɗauko Tsohon Kwamishinansa, Ya Naɗa Shi a Shirgegen Muƙami

Tinubu Ya Sake Ɗauko Tsohon Kwamishinansa, Ya Naɗa Shi a Shirgegen Muƙami

  • Bola Ahmed Tinubu ya amince da naɗin Mr. Olatunji Bello a matsayin babban jami'im hukumar kula da abokan ciniki ta ƙasa (FCCPC)
  • Mai magana da yawun shugaban kasa, Ajuri Ngelale ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin, 24 ga watan Yuni, 2024
  • Wannan ne karo na biyu da shugaba Bola Tinubu ya naɗa tsohon kwamishinan jihar Legas a cikin wata ɗaya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya amince da naɗin Mr. Olatunji Bello a matsayin shugaban hukumar FCCPC ta ƙasa.

Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Ajuri Ngelale ne ya tabbatar da wannan naɗi a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin, 24 ga watan Yuni, 2024.

Kara karanta wannan

Gwamma ya faɗi gaskiya kan shirin tsige Mai aAfarma Sarkin Musulmi a Najeriya

Shugaba Tinubu.
Bola Tinubu Ya Nada Bello a Matsayin Sabon Shugaban Hukumar FCCPC Hoto: @DOlusegun16
Asali: Twitter

Dada Olusegun, mai taimakawa shugaban ƙasa na musamman kan harkokin soshiyal midiya ya wallafa sanarwar a shafinsa na manhajar X wanda aka fi sani da Twitter.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Taƙaitaccen bayani kan Bello

Mista Bello ƙwararren lauya ne kuma fitaccen dan jarida, sannan ya taɓa riƙe sakataren gwamnatin jihar Legas.

Sabon shugaban FCCPC ya kammala digirinsa na biyu a fannin shari'a da diflomasiyya a jami'ar jihar Legas.

Olatunji Bello ya yi karatun lauya a jami'ar jihar Legas kuma ya samu shaidar zama cikakken lauya a 2002.

Wani sashen sanarwar ta ce:

"Shugaban ƙasa na fatan sabon shugaban wannan hukuma mai muhimmanci zai yi amfani da gogewarsa wajen yiwa al'umma hidima da tabbatar da tsare haƙƙin abokan hulɗa a Najeriya.

Sanarwar ta ƙara da cewa Bello ya fara aikin jarida ne a jaridar Concord a shekarar 1985 kuma ya rike mukamai da dama.

Kara karanta wannan

Matsin rayuwa: Tinubu ya shawarci 'yan Najeriya kan yadda za su samu abinci cikin sauki

Mukaman da ya riƙe sun haɗa da editan ɓangaren siyasa, editan Sunday Concord da kuma babban editan jaridar Concord na kasa.

Ya kuma taba rike mukamin kwamishinan muhalli a karkashin gwamnatoci daban-daban a jihar Legas.

Tinubu ya ba ƴan Najeriya shawara

A wani rahoton kuma Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya shawarci ‘yan Najeriya kan yadda za a shawo kan tsadar kayan abinci a kasar.

Ta bakin hadiminsa, ya ce akwai bukatar kowa ya natsu ya ba da gudunmawa wajen gina kasa, musamman duba da yanayin da ake ciki.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262