Jirgi Ya Gamu da Hatsari Ana Tsaka da Ruwan Sama, Mutane Sun Mutu a Arewa

Jirgi Ya Gamu da Hatsari Ana Tsaka da Ruwan Sama, Mutane Sun Mutu a Arewa

  • Jirgin ruwa ɗauke da masunta ya yi hatsari a ƙauyen Kippo da ke ƙaramar hukumar Mokwa a jihar Neja ranar Alhamis da ta wuce
  • Ma'aikatar jin kai da magance bala'o'i ta jihar Naja ta ce mutum biyu ƴan gida ɗaya sun mutu a haɗarin kuma an ciro gawar ɗaya daga ciki
  • Haka nan kuma wasu ƴan bindiga sun kai hari kauyuka da dama a ƙaramar hukumar Shiroro, sun raba mutane da gidajensu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Niger - Wasu mutum biyu ‘yan uwan juna sun rasa rayuwarsu yayin da wani jirgin ruwa ya kife a ruwa a kauyen Kippo da ke karamar hukumar Mokwa a jihar Neja.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai ƙazamin hari kan bayin Allah, sun kashe rayuka da yawa a Arewa

Habibu Wushishi, daraktan yada labarai da dabaru a ma’aikatar jin kai da magance bala’o’i na jihar ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi a Minna.

Taswirar jihar Neja.
Masunta yan gida ɗaya sun mutu a hatsarin jirgin ruwa a jihar Neja
Asali: Original

Wushishi ya bayyana cewa jirgin ya yi hatsari ne da misalin ƙarfe 10:00 na daren ranar Alhamis, 20 ga watan Yuni, 2024, kamar yadda Premium Times ta kawo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce waɗanda hatsarin ya rutsa da su masunta ne kuma sun fito sana'arsu ne lokacin da jirgin ya nutse da su.

Yadda jirgin ruwa ya nutse a Neja

"Masuntan suna cikin kamun kifi a kogin Niger yayin da kwale-kwalen ya kife da su saboda tsananin ruwan saman da ke sauka tare da iska mai ƙarfi.
"Zuwa yanzun mun tsamo gawar ɗaya daga cikinsu kuma ana ci gaba da aiki ba kama hannun yaro domin ciro gawar ɗayan masuncin da haɗarin ya rutsa da shi," in ji Wushishi.

Kara karanta wannan

Sarautar Kano: Gingima-gingiman lauyoyi sun soki hukuncin kotu, sun zargi ƴan siyasa

Ƴan bindiga sun shiga kauyukan Niger

A gefe guda kuma Wushishi ya ce wasu ‘yan bindiga sun kai hari a kauyukan Lanta, Tunga, Dnakau da Juweedna da ke yankin Erena a karamar hukumar Shiroro.

Ya ce ƴan bindigar sun kai hare-haren ne da misalin karfe 5:30 na yammacin ranar 20 ga watan Yuni, rahoton Daily Post.

A cewarsa, ‘yan bindigar sun yi awon gaba da shanu da tumaki da yawa tare da lalata gidaje da dama, inda sama da mutane 600 suka rasa matsuguni.

Ya ce a halin yanzu ‘yan gudun hijira daga kauyukan da lamarin ya shafa na samun mafaka a sansanonin ‘yan gudun hijira na Erena da Kuta.

Ƴan bindiga sun kai farmaki a Katsina

A wani rahoton kun ji cewa yan bindiga sun kai mummunan hari garin Maidabino da ke ƙaramar hukumar Ɗanmusa a jihar Katsina, sun kashe bayin Allah.

Kara karanta wannan

Ana cikin rikicin sarauta gwamnatin Abba ta aika da gargadi ga al'ummar Kano

Mazauna garin sun bayyana cewa yawan ƴan bindigar ya sa babu jami'in tsaron da ya iya tunkararsu, sun kuma tafi da mutane 50.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262