Ana Tsaka da Rikicin Sarauta, Ganduje Ya Yi Babban Rashi a Jihar Kano
- Allah ya yiwa surukar Ganduje, Hajiya Asiya Muhammad Gauyama rasuwa da safiyar ranar Litinin, 24 ga watan Yuni, 2024
- Ofishin shugaban APC na kasa ya sanar da cewa za a yi janazar Hajiya Asiya, mahaifiyar Gwaggo a gidan Abdullahi Ganduje da ke Kano da misalin karfe 2:00 na rana
- Wannan na zuwa ne kwana ɗaya bayan rasuwar surukar mataimakin shugaban ƙasa, Sanata Kashim Shettima
Jihar Kano - Shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na ƙasa, Dokta Abdullahi.Umar Ganduje ya yi babban rashi a jihar Kano.
Surukar Ganduje, Hajiya Asiya Muhammad Gauyama, ta riga mu gidan gaskiya da sanyin safiyar yau Litinin, 24 ga watan Yuni, 2024.
Mai magana da yawun shugaban APC na ƙasa, Edwin Olofu ne ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a Abuja, kamar yadda The Nation ta ruwaito.
Sanarwar ta bayyana marigayya Hajiya Asiya a matsayin mace mai ƙima wadda ta ƙarar da rayuwarta wajen taimakom ƴan uwanta, al'umma da kuma addini.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yashe za a yi janazar mahaifiyar Gwoggo?
Za a yi mata Sallar jana'iza a yau Litinin da misalin ƙarfe 2:00 na rana a gidan Dr. Abdullahi Umar Ganduje da ke kan titin Miyangu a jihar Kano.
Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, kakakin Ganduje ya ce:
"Cikin jimami muna sanar da rasuwar Hajiya Asiya Muhammad Gauyama, mahaifiyar Farfesa Hafsatu Abdullahi Umar Ganduje, matar shugaban APC, Dakta Abdullahi Ganduje CON."
"Muna addu'ar Allah SWT ya jikan Hajiya Asiya Muhammad Gauyama ya sa ta huta, ya kuma bai wa iyalai da masoyanta hakurin jure rashinta.
Surukar Kashim Shettima ta rasu
Wannan na zuwa ne sa'o'i 24 bayan mataimakin shugaban ƙasa, Sanata Kashim Shettima ya yi rashin surukarsa.
Maryam Abubakar-Albishir, surukar Shettima ta rasu ne a Kano ranar Lahadi, 24 ga watan Yuni bayan fama da jinya ta tsawon lokaci.
Za a yi jana'izar Maryam Abubakar, mahaifiyar matar mataimakin shugaban kasa, Nana Shettima, ranar Litinin a Kano kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
Kotu ta ɗage ƙarar gwamnatin Kano
A wani rahoton kun ji cewa Yayin da ake ci gaba da rigima kan kujerar sarautar Kano, kotu ta ɗage zaman ƙarar da gwamnatin Kano ta kai kan tsige Aminu Ado Bayero.
Mai Shari'a Amina Adamu Aliyu ta ɗage ƙarar da aka nemi hana Aminu da sarakuna hudu ayyana kansu a matsayin sarakuna zuwa 2 ga watan Yuli.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng