Babbar Kotu Ta Ɗauki Mataki a Shari'ar Tsige Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero
- Yayin da ake ci gaba da rigima kan kujerar sarautar Kano, kotu ta ɗage zaman ƙarar da gwamnatin Kano ta kai kan tsige Aminu Ado Bayero
- Mai Shari'a Amina Adamu Aliyu ta ɗage ƙarar da aka nemi hana Aminu da sarakuna hudu ayyana kansu a matsayin sarakuna zuwa 2 ga watan Yuli
- Wannan dai na zuwa ne bayan Gwamna Abba Kabir ya rusa masarautu biyar kuma ya dawo da Muhammadu Sanusi II
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kano - Babbar kotun jihar Kano ta ɗage zaman sauraron shari'ar da ke gabanta kan rushe masarautu biyar da tsohon gwamnan jihar ya kirkiro.
A karar an roƙi babbar kotun jihar ta haramtawa Aminu Ado Bayero da sauran sarakuna hudu ayyana kansu a matsayin halastattun sarakuna.
Kamar yadda jaridar Punch ta kawo rahoto yau Litinin, 24 ga watan Yuni, kotun ta ɗauki matakin ɗage zaman shari'ar zuwa ranar 2 ga watan Yulo, 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mai shari'a Amina Adamu Aliyu ce take jagorantar shari'ar masarautar Kano a babbar kotun jiha, kamar yadda NTA News ta ruwaito.
Gwamnatin Kano ta maka Aminu a kotu
Gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ce ta shigar da ƙarar domin hana Aminu Bayero bayyana kansa a matsayin Sarkin Kano.
Tun farko dai gwamnatin Kano ta yi bayanin cewa tsohon gwamna, Abdullahi Ganduje ya naɗa Aminu Ado a matsayin sarkin kananan hukumomi takwas na cikin birni.
A cewarta, naɗin Aminu Ado bai shafi duka kananan hukumomin Kano guda 44 illa dai cikin birni ne kaɗai a karƙashinsa.
Idan ba ku manta ba, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya tuɓe Aminu Ado da sarakuna 4 daga matsayin sarakuna bayan ya sa hannu a dokar masarauta, 2024.
Duk da haka, Sarki na 15 ya ƙi barin ƙaramar fadar Nasarawa kuma ya ƙalubalanci matakin Gwamna Abba a gaban ƙuliya.
Yan sanda sun kara tsaro a fada
Kun ji cewa rundunar ƴan sandan jihar Kano ta fito ta yi magana kan dalilin da ya sanya aka ga ƙarin jami'an tsaro a fadar Muhammadu Sanusi II da Aminu Ado Bayero
Kwamishinan ƴan sandan jihar mai barin gado, AIG Usaini Gumel, ya bayyana cewa an tura ƙarin jami'an tsaron ne domin samar da tsaro a wuraren guda biyu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng