'Yan Bindiga Sun Kai Kazamin Hari Kan Bayin Allah, Sun Kashe Rayuka da Yawa a Arewa

'Yan Bindiga Sun Kai Kazamin Hari Kan Bayin Allah, Sun Kashe Rayuka da Yawa a Arewa

  • Ƴan bindiga sun kai mummunan hari garin Maidabino da ke ƙaramar hukumar Ɗanmusa a jihar Katsina, sun kashe bayin Allah
  • Mazauna garin sun bayyana cewa yawan ƴan bindigar ya sa babu jami'in tsaron da ya iya tunkararsu, sun kuma tafi da mutane 50
  • Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ƴan sandan jihar ASP Abubakar Sadiq Aliyu ya ce tuni suka fara gudanar da bincike

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Katsina - Adadi mai yawa na ƴan bindiga ɗauke da mugayen makamai sun tarwatsa garin Maidabino, gari na uku mafi girma a ƙaramar hukumar Ɗanmusa a Katsina.

Maharan sun kashe kusan mutane tara a harin, kuma sun yi garkuwa da wasu mutum 50 waɗanda galibi mata ne da ƙananan yara.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai ƙazamin farmaki kan bayin Allah, sun kashe jami'an tsaro

Gwamna Malam Dikko Radda.
'Yan bindiga sun halaka mutane da dama a garin Maidabino da ke Katsina Hoto: Dr. Dikko Umaru Radda
Asali: Facebook

Wani mazaunin Maidabino ya tabbatarwa Daily Trust cewa ƴan bindigar sun ɗauki sa'o'i suna cin karensu babu babbaka ba tare da an tanka masu ba saboda yawansu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴan bindiga sun yi ɓarna a Katsina

Ya ce sama da gidaje 10 da shaguna 15 da motoci akalla tara ne ‘yan ta’addan suka kona a mummunan harin na ranar Asabar zuwa wayewar garin Lahadi.

Mutumin ya ce ƴan bindigar sun shiga garin tun karfe 10:00 na daren ranar Asabar har zuwa karfe 2:30 na wayewar garin Lahadi.

A rahoton Leadership, ganau ya ce:

"Abin da ya faru tun farko shi ne, ranar Jumu'a, sojoji sun rako kusan motoci 30 na ƴan kasuwa da suka dawo daga kasuwar Ƴantumaki, kwatsam suka ci karo da ƴan bindiga a titin zuwa Maidabino.
"Sojojin sun yi nasarar kashe wasu ƴan bindigar a musayar wuta, hakan ya sa suka koma suka haɗa ƴan uwansu ƴan bindiga da yawa ta yadda sojojin ba za su iya tunkarar su ba.

Kara karanta wannan

Sarkin Musulmi ya fadi lokacin da za a kawo karshen matsalar rashin tsaro a Arewa

Ƴan sanda sun fara binciken harin ƴan bindiga

Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ƴan sandan jihar Katsina, ASP Abubakar Sadiq Aliyu ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai.

Kakakin ƴan sandan ya ce mutum 7 aka kashe a harin kuma yanzu haka jami'an tsaro sun fara bincike kan lamarin.

Wani mazaunin Maidabino ya shaidawa Legit Hausa cewa ba ƙaramar ɓarna ƴan bindiga suka yi masu ba kuma sama awanni 4 babu jami'an tsaron ɗa suka kawo masu agaji.

Mutumin ya ce:

"Muna cikin jimami da tashin hankali, Allah ya saka mana. Ƴan bindiga da yawa sun haura 100 sukan shigo da daddare, suka kashe mana ƴan uwa, suka kona mana dukiya.
"Sun mana ɓarna da yawan gaske sai dai Allah ya bi mana haƙkinmu. Sun ɗauki tsawon lokaci kamar yadda kuka faɗa suna aikata mugun nufinsu, jami'an tsaro b asu zo ba."

Nasarorin sojoji kan ƴan bindiga a mako 1

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun shiga har cikin fadar babban basarake sun tafka barna

Kuna da labarin cewa Dakarun sojojin Najeriya na ci gaba da kai samame kan ƴan bindiga da sauran masu aikata miyagun laifuka a faɗin ƙasar nan.

Hedkwatar tsaro (DHQ) ta ce sakamakon haka sojojin sun yi nasarar hallaka ƴan ta'adda 220, sun kamo wasu 395 tare da ceto mutanen da aka sace.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262