Sanusi II vs Bayero: Manazarci Ya Hango Makomar Sarautar Kano Bayan Hukuncin Kotu

Sanusi II vs Bayero: Manazarci Ya Hango Makomar Sarautar Kano Bayan Hukuncin Kotu

  • An yi kakkausar suka kan rigimar masarautar Kano da ake yi wadda ta kai ga zuwa gaban kotu bisa zargin ta nakasa sarautar gargajiya
  • Wani mai sharhi kan al'amuran yau da kullum, Okanlawon Gaffar ya ce sarauta wani matsayi ne da ta samo asali daga al'ada da shugabanci
  • Mista Gaffar ya koka kan rikicin sarautar Kano, inda ya ce abin da ke faruwa yanzu zai ba gwamnoni damar tsige sarakunan da ba su so

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

An bayyana hukuncin kotu na baya-bayan nan kan rikicin sarautar Kano a matsayin cusa shari'a a harkar sarauta wanda ya sabawa tsarin al'adar masarauta kasar.

A wata tattaunawa ta musamman da Legit.ng ta yi da wani mai fashin baki, Okanlawon Gaffar, ya ce tun farko bai kamata a kai lamarin kotu ba.

Kara karanta wannan

Rusa fadar Nasarawa: Gwamnatin Abba ta ba Aminu Bayero sabon umarni a Kano

Manazarci ya yi magana kan rikicin sarautar Kano
Manazarci na fargabar gwamnan Kano na gaba zai iya tsige sarki na lokacin. Hoto: @Imranmuhdz, @Kyusufabba
Asali: Twitter

Mai sharhi kan al'amuran yau da kullum ya ce yana fargabar wannan rigimar ta sarautar Kano za ta bude wa gwamnoni kofar tsige sarakuna a duk lokacin da suka ga dama.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A baya ne muka ruwaito cewa Gwamna Abba Yusuf na jihar Kano ya tsige Aminu Ado Bayero tare da mayar da Muhammadu Sanusi II kan sarautar Kano, abin da ya kai ga zuwa kotu.

Mahangar Gaffar kan matsayin sarki a Najeriya

A mahangar Mista Gaffar, kujerar sarki na wakiltar wani nauyin shugabanci na daban, wanda al'ada da kyawawan dabi'u ke zaben wanda zai hau wannan kujera.

A cewar sa:

"Kai tsaye an shari'antar da tsarin sarautar gargajiya la'akari da rikicin sarautar Kano inda kotu ke kokarin zabar wanda zai zamarwa al'umma sarki.
"Idan har gwamna zai tsige sarki ya naɗa wani, me zai hana gwamna na gaba shi ma ya tsige sarki ya naɗa wani? A halin yanzu masarauta ta koma abar kaskantarwa."

Kara karanta wannan

Sanusi II Vs Aminu: Lauya ya fadawa Abba yadda zai kawo karshen rikicin sarautar Kano

'Yan sanda sun mamaye fadar sarkin Kano

A safiyar yau Litinin muka ruwaito cewa jami'an rundunar 'yan sandan Najeriya sun mamaye fadar mai martaba sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II.

Mamaye fadar ya biyo bayan fatattakar'yan tauri da ke tsaron Sanusi II da 'yan sandan suka yi, a wani yunkuri na zargin za a mayar da Aminu Bayero kujerarsa ta sarki.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.