Dubi jerin gidajen jaridu da kafafen yada labarai da Boko ta yi alkawarin kaiwa hari
- Kungiyar Boko Haram ta yi alkawarin kai hari kan wasu gidajen jaridun Najeriya
- Ta ce tana da dalilin kai hare-haren
- Shugaban kungiyar Boko Haram, Shekau, ya fadi hakan a wani sabon faifan bidiyo
A wani sabon faifan bidiyo da kungiyar Boko Haram ta fitar a jiya Laraba, shugaban kungiyar, Abubakar Shekau, ya ce zasu kai hare-hare a kan wasu manyan gidajen jaridun kasar nan.
Kungiyar ta ce tana da dalilin kai hari a kan kowanne daga cikin gidajen jaridun. A misalin da kungiyar ta bayar, ta bayyana cewar zata kai hari kan gidan jaridar Thisday ne saboda an taba amfani da gidan jaridar wajen yin batanci ga Manzon Allah a shekarar 2002.
DUBA WANNAN: Ban yarda Ubangiji zai yi farinciki da kisan bayinsa ba - Buhari
Ragowar gidajen jaridu da kafafen yada labarai da kungiyar ta ci alwashin kaiwa hari sun hada da; Sahara Reporters, VOA Hausa, rfi Hausa, Punch, Daily Sun, Vanguard, The Nation, Tribune, da National Accord.
Kungiyar ta zargi jaridun da kafafen yada labaran da yin karairayi a kansu da kuma raini da cin mutuncin Musulmi.
Kungiyar ta ce wadannan laifuka ne da ba zata yafe ba.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng