Shugaba Tinubu Ya Umarci a Hukunta Wasu Ma'aikatan Najeriya, Ya Fadi Laifinsu

Shugaba Tinubu Ya Umarci a Hukunta Wasu Ma'aikatan Najeriya, Ya Fadi Laifinsu

  • Shugaban ƙasa Bola Ahmed ya nuna takaicinsa kan yadda wasu ma'aikatan gwamnati da suka koma ƙasar waje ke ci gaba da karɓar albashi
  • Shugaba Tinubu ya umarci cewa a tabbatar ma'aikatan sun mayar da kuɗaɗen da suka karɓa zuwa asusun gwamnati
  • Tinubu ya kuma umarci a hukunta shugabannin hukumomi da suka taimaka ma'aikatan suka riƙa aikata wannan badaƙalar

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya bayar da umarnin cewa duk ma’aikatan gwamnati da ke karɓar albashi daga gwamnati bayan sun koma ƙasashen waje su mayar da kuɗaɗen.

Shugaban ƙasan ya kuma bayar da umarnin a hukunta shugabanin hukumomin da suka taimaka musu suka aikata wannan badaƙalar.

Kara karanta wannan

Ana cikin rikicin sarauta gwamnatin Abba ta aika da gargadi ga al'ummar Kano

Tinubu ya umarci a hukunta ma'aikata
Shugaba Tinubu ya umarci a hukunta ma'aikata da ke karbar albashi duk da sun koma kasar waje Hoto: @DOlusegun
Asali: Facebook

Tinubu ya ba da umarnin ne a ranar Asabar a wajen ba da lambobin yabo da ofishin shugaban ma’aikatan gwamnatin tarayya (HOCSF) ya shirya domin tunawa da makon ma’aikata na 2024, cewar rahoton jaridar Tribune.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Taron kuma an yi shi ne don karrama wasu fitattun ma’aikatan gwamnati a manyan ma’aikatu, rahoton jaridar Daily Trust ya tabbbatar.

Me Tinubu ya ce kan ma'aikatan bogi?

Shugaba Tinubu wanda ya samu wakilcin Sanata George Akume, sakataren gwamnatin tarayya (SGF), ya nuna rashin jin daɗinsa kan halin ma’aikatan bogi.

"Na yi mamaki matuƙa da bayanan da shugabbar ma'aikata ta yi dangane da ma'aikatan da suka koma ƙasashen wajen amma suna karɓar albashi ba tare da sun yi murabus a hukumance ba."
"Na ji daɗi cewa an ɗauki matakai domin magance wannan matsalar, amma dole mu tabbatar da cewa masu hannu a ciki an hukunta su kuma sun dawo da abin da suka karɓa."

Kara karanta wannan

An miƙa wa Bola Tinubu sunan wanda ya kamata ya naɗa a matsayin ministan jin ƙai

"Dole ne a sanya masu laifin su mayar da kuɗaɗen da suka karɓa ta hanyar zamba."

- Bola Tinubu

An gano ma'aikatan bogi

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ta yi nasarar gano ma’aikatan bogi da ke zaune a kasashen ketare amma suna karbar albashi daga gwamnatin Najeriya.

Shugabar ma’aikata ta ƙasa, Dr. Folasade Yemi Esan ce ta bayyana cewa an gano ma’aikatan ne bayan binciken tsarin biyan albashi na IPPIS a kwanan nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng