Ana Cikin Rikicin Sarauta Gwamnatin Abba Ta Aika da Gargadi Ga Al'ummar Kano

Ana Cikin Rikicin Sarauta Gwamnatin Abba Ta Aika da Gargadi Ga Al'ummar Kano

  • Ma'aikatar lafiya ta jihar Kano ta gargaɗi al'ummar jihar da su guji shan ruwan sama domin hana yaɗuwar cutar amai da gudawa
  • A cikin wata sanarwa da ma'aikatar lafiyan ta fitar ta buƙaci al'ummar jihar da riƙa tsaftace abubuwan sha da na ci kafin su yi amfani da su
  • Hakan na zuwa ne dai bayan an samu ɓullar cutar amai da guduwa a wasu sassan ƙasar nan a cikin ƴan kwanakin nan

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Gwamnatin jihar Kano ta shawarci jama’a da su guji shan ruwan sama domin hana yaduwar cutar amai da gudawa saboda shigar damina.

Wannan kiran dai na zuwa ne yayin da cutar amai da gudawa ta yaɗu a wasu sassan ƙasar nan, cewar rahoton jaridar The Punch.

Kara karanta wannan

Ana tsaka da rikicin sarauta, ƴan bindiga sun kai hari Masallaci, sun sace basarake

Gwamnatin Kano ta yi gargadi kan cutar kwalara
Gwamnatin Kano ta bukaci Kanawa su guji amfani da ruwan sama Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Twitter

Shawarar na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban sashin hulɗa da jama’a na ma’aikatar lafiya, Ibrahim Abdullahi ya rabawa manema labarai a ranar Asabar, cewar rahoton jaridar Tribune.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ibrahim Abdullahi ya ce shawarar ta zama dole domin yawanci lokacin damina na zuwa da matsalolin cutar amai da guduwa wacce tuni ta ɓulla a wasu jihohin ƙasar nan.

"Ya zama wajibi a faɗakar da jama'a cewa rigakafi yafi magani. Ya kamata mutane su lura da abin da suke ci musamman kayan lambu, kayan itatuwa da ruwan sha."
"Ya kamata mutane su yi hattara a kan hakan domin su kiyaye kansu daga gurɓataccen abinci ko ruwan sha."
"Yana da kyau mutane su fahimci cewa ruwan sama a farkon damina ba shi da tsafta. Idan har sai an yi amfani da shi, dole ne a tsaftace shi ta hanyar tafasa shi da tacewa kafin a yi amfani da shi."

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun yi magana yayin da kotu ke shirin sanar da halataccen Sarkin Kano

"Hakan zai taimaka wajen kiyaye mutane daga kamuwa da cutar amai da gudawa."

- Ibrahim Abdullahi

Batun cutar kwalara a Legas

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Lagos ta yi martani bayan mutane 24 sun mutu saboda cutar kwalara da ta ɓarke a jihar.

Ana zargin wadanda suka kamu da cutar sun sha kunun aya ne wanda yake da matsala a karamar hukumar Eti-Osa a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng