"Ku Mayar da Ni Gida": Yahaya Bello Ya Nemi Alfarma 1 Wajen EFCC, Ya Jero Dalilai

"Ku Mayar da Ni Gida": Yahaya Bello Ya Nemi Alfarma 1 Wajen EFCC, Ya Jero Dalilai

  • Yayin da ake ci gaba da tuhumar Yahaya Bello kan badakala, ya nemi alfarma guda daya wajen hukumar EFCC a Abuja
  • Tsohon gwamnan Kogi ya ce bai kamata a ci gaba da tuhumarsa a Abuja ba tun da ba a can ya aikata abin da ake zarginsa ba
  • Ya roki hukumar EFCC da ta dawo da shi jihar Kogi domin ci gaba da tuhumar da ake yi masa madadin tsare a birnin Abuja

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kogi - Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya nemi alfarma wajen hukumar yaki da cin hanci ta EFCC.

Alhaji Yahaya Bello ya roki hukumar EFCC da ta dawo da shi jihar kogi domin ci gaba da tuhumarsa a can.

Kara karanta wannan

"Ban san Aminu Ado ba": Kwamishinan 'yan sanda ya fadi matsayarsa kan rigimar Kano

Yahaya Bello ya roki hukumar EFCC ta dawo da shi jihar Kogin
Yahaya Bello ya nemi alfarma a dawo da bincikensa jihar Kogi. Hoto: Yahaya Bello, Economic and Financial Crimes Commission.
Asali: Twitter

Kogi: Yahaya Bello ya roki EFCC alfarma

Tsohon gwamnan ya bayyana haka ne ganin cewa a jihar ya aikata abin da ake zarginsa a kai, kamar yadda TVC News ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lauyan Yahaya Bello, Adeola Adedipe shi ya yi wannan roko ga hukumar domin saukaka binciken nata da take yi, cewar Daily Post.

Adeola ya ce tun da tsohon gwamnan ya aikata abin da ake zarginsa a jihar ne lokacin da yake gwamna, ya kamata a ci gaba da rike shi a can.

Ya ce ya fi dacewa a ci gaba da rike shi a jihar Kogi inda ake zarginsa madadin tsare shi a birnin Abuja.

Zargin da EFCC ke yi kan Yahaya Bello

Hakan ya biyo bayan zargin badakalar N80bn da ake yiwa tsohon gwamnan lokacin da yake mulkin jihar.

Sai dai tsohon gwamnan ya ki gurfana a gaban kotu har sau hudu inda ya ke ba da uzuri kan rashin halartar tasa.

Kara karanta wannan

Malamin Musulunci ya kunyata 'yan siyasa a zaman makokin tsohon gwamna

Daga ciki akwai nuna wariya da hukumar ta EFCC ke yi masa a Abuja ba tare da wani dalili ba.

Jigon PDP ya gano maboyar Yahaya Bello

A wani labarin, kun ji cewa babban jigon jam'iyyar PDP, Austin Okai, ya fallasa wurin da tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya ɓuya domin kaucewa kamen EFCC.

Mista Okai ya bayyana cewa yanzu haka Yahaya Bello na cikin gidan gwamnatin Kogi da ke birnin Lokoja ya ɓuya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.