Yan Sanda Sun Tura Sako Bayan Kisan Wanda Ya Ƙirkiro Addini a Bauchi

Yan Sanda Sun Tura Sako Bayan Kisan Wanda Ya Ƙirkiro Addini a Bauchi

  • Rundunar yan sandan Najeriya a jihar Bauchi ta tura muhimmin sako ga al'umma bayan kisan matashin da ya kirkiro addini
  • Kwamishinan 'yan sanda a jihar, CP Auwal Musa Muhammad ne ya yi kiran ga daukacin al'umma domin kwantar da hankali
  • CP Auwal Musa Muhammad ya yi karin haske kan matakin bincike da rundunar ta dauka domin kaucewa faruwar lamarin a gaba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Bauchi - Rundunar 'yan sanda a jihar Bauchi ta yi kira na musamman ga al'umma bayan an kashe matashin da ake zargi da kirkiro sabon addini.

An zargin matashin mai suna Usman da fara yaɗa addinin da yake kira 'Fera Movement' a kauyen Nasaru da ke jihar Bauchi.

Kara karanta wannan

Yadda kwankwaɗar kunun aya ya hallaka mutane 24, Gwamna ya dauki mataki mai tsauri

Jihar Bauchi
Yan sanda sun yi kira ga iyaye bayan kisan matashi a Bauchi. Hoto: Nigeria Police Force Bauchi State Command
Asali: Facebook

Legit ta gano bayanan da yan sanda suka yi ne a cikin wani sako da rundunar ta wallafa a shafinta na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan sanda: A kwantar da hankali

Kwamishinan 'yan sanda a jihar Bauchi, CP Auwal Musa Muhammad ya yi kira ga al'umma da su kwantar hankulansu kan lamarin.

CP Auwal Musa Muhammad ya kara da cewa al'ummar jihar su cigaba da harkokinsu na yau da kullum ba tare da jin tsoron wata barazana ba.

'Yan sanda: A guji daukan doka a hannu

Har ila yau, CP Auwal Musa Muhammad ya yi kira ga al'ummar jihar kan kaucewa daukar doka a hannu idan an samu sabani.

Kwamishinan ya ce abin da ya kamata mutane su rika yi shi ne hada kai da jami'an tsaro idan lamari irin wannan ya faru ba daukar doka a hannu ba.

Kara karanta wannan

Yadda aka kashe matashi yana ƙoƙarin tallata sabon addini a Arewacin Najeriya

Yan sanda sun yi kira ga al'umma

Rundunar ta yi kira ga iyaye da sauran al'umma kan zuba ido wajen ganin sun hana wadanda suke ƙarƙashinsu yin ba daidai ba idan lamari irin wannan ya faru.

CP Auwal Musa Muhammad ya kuma tabbatar da cewa za su sanar da sakamakon bincike da suke kan lamarin da zarar sun kammala.

An kashe mahauci kan rikicin addini

A wani rahoton, kun ji cewa wasu mutane sun yi ajalin wani mahauci mai suna Usman Buda wanda ake zargin ya yi batanci ga Annabi Muhammad (SAW).

Wani jami'in tsaro da ya bukaci a boye sunansa ya bayyana cewa marigayin yana zama ne a Gidan Igwe da ke karamar hukumar Sokoto ta Arewa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Online view pixel