Ana Tsaka da Rikicin Sarauta, Ƴan Bindiga Sun Kai Hari Masallaci Sun Sace Basarake

Ana Tsaka da Rikicin Sarauta, Ƴan Bindiga Sun Kai Hari Masallaci Sun Sace Basarake

  • Mahara sun yi garkuwa da wani mai riƙe da sarauta, Madakin Shabu Musa Shu'aibu jim kaɗan bayan ya fito daga masallaci a Nasarawa
  • Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ƴan sandan jihar, Rahman Nansel ya ce tuni dakarun ƴan sanda suka bazama domin ceto mutumin
  • Ganau sun bayyana cewa maharan sun buɗe wuta domin tsorata mutane, kana suka yi awon gaba da Madaki a daren ranar Alhamis

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Nasarawa - Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da wani mai rike da sarautar gargajiya a jihar Nasarawa, Madakin Shabu, Musa Shuaibu.

Maharan sun yi awon gaba da basaraken ne jim kaɗan bayan ya fito daga Masallaci ranar Alhamis da ta gabata, 20 ga watan Yuni, 2024 da daddare.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun kashe ƴan bindiga 220, sun ƙwamuso wasu sama da 300 a Najeriya

Sufetan yan sanda, IGP Kayode.
Yan bindiga sun yi garkuwa da mai rike da sarauta a jihar Nasarawa Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Twitter

Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ƴan sanda ta jihar Nasarawa, DSP Rahman Nansel ya tabbatar da faruwar lamarin ga Channels tv.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wane mataki ƴan sanda suka ɗauka?

A cewarsa, an yi garkuwa da Shuaibu ne a daren ranar Alhamis bayan ya yi Sallah a wani Masallaci da ke kusa da gidansa a Shabu.

Ya kara da cewa dakarun ƴan sanda na ci gaba da kokarin kubutar da mutumin tare da damke wadanda suka aikata laifin domin gurfanar da su a gaban kuliya.

Lamarin wanda ya faru da misalin karfe 08:00 na daren ranar Alhamis ya jefa mazauna yankin cikin tashin hankali yayin da maharan suna buɗe wuta a iska.

Yadda mahara suka sace Madakin Shabu

Ganau sun shaidawa jaridar Vanguard cewa an yi garkuwa Madakin Shabu ne ‘yan mintuna kadan bayan Sallar isha’i a masallacin Shabu a gefen babban titi.

Kara karanta wannan

Sojoji sun cafke masu garkuwa da mutane da suka addabi Taraba, sun ba da bayanai

A cewar ganau, masu garkuwan sun zo da shirin kashe duk wanda ya kawo masu cikas, lamarin da ya sa sauran masallata da ‘yan kasuwa suka tsere cikin tsoro.

Lamarin tsaro na ƙara taɓarɓarewa a yankin duk da matakin taƙaita zirga-zirga daga faɗuwar rana zuwa wayewar gari da aka ɗauka da nufin dawo da zaman lafiya.

Ƴan bindiga sun kashe amarya

A wani rahoton kuma mahara sun yi ajalin amarya mako ɗaya da ɗaura mata aure gabanin ta tare gidan mijinta a jihar Anambra ranar Litinin.

Lamarin ya faru ne yayin da ƴan bindiga masu tilasta bin dokar zaman gida suka kai farmaki kauyuka biyu, inda suka kashe mutane da yawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262